Karin bayanai: Allah ya yiwa wani tsohon sanatan Najeriya rasuwa

Karin bayanai: Allah ya yiwa wani tsohon sanatan Najeriya rasuwa

Dan siyasar jamhuriya ta biyu, Sanata Francis Arthur Nzeribe, haifaffen garin Oguta, ya rasu yana da shekaru 83.

Wata majiya mai karfi ta kusa da danginsa da ta zanta da jaridar Punch tare da neman a boye sunanta da yammacin ranar Lahadi ta ce dan siyasar ya mutu ne a wani asibiti a kasar waje.

Iyalan sun tabbatar da mutuwar dan siyasar a wata sanarwa da suka fitar ranar Lahadi, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Marigayi Francis Arthur ya rasu
Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa wani tsohon sanatan Najeriya rasuwa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Abin da ya kamata ku sani game da Sanata Francis Arthur Nzeribe

1. An haifi Arthut Nzeribe a ranar 2 ga watan Nuwamban 1938 , ya yi sallama da duniya a ranar 8 ga watan Mayun bana; 2022

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

2. Matarsa ta biyu ita ce kanwar Hajiya Asabe Yar’adua, matar marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’aduwa, wanda dan’uwan Shugaba Umaru ‘Yar’adua ne,

3. Ya shiga harkar siyasa, inda ya zama Sanata mai wakiltar mazabar Orlu a jihar Imo daga Oktoba 1983 zuwa Disamba 1983 da Mayu 1999 zuwa Mayu 2007 a jam'iyyar PDP a wancan lokacin.

4. A watan Agustan 2007 aka nada Nzeribe mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, kamar yadda AllAfrica ta wallafa a shekarun baya.

5. Bayar 'yar rashin lafiya, ya rasu a asibitin kasar waje, kamar yadda rahotanni da majiyoyi suka tabbatar.

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Tsohon ministan sadarwa na Najeriya ya mutu

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel