Yadda rahotanni suka kusa jefa rayuwar Ramatu Abarshi da diyarta da aka sace a cikin hatsari - Majiya

Yadda rahotanni suka kusa jefa rayuwar Ramatu Abarshi da diyarta da aka sace a cikin hatsari - Majiya

  • Yan uwan Ramatu Abarshi, mai aikin taimakon jama’a da yan bindiga suka sace sun koka kan halin da ake ciki
  • Sun bayyana cewa ba za su yi sharhi kan lamarin ba domin labaran soshiyal midiya sun kusa jefa rayuwar Ramatu da na diyarta a hatsari
  • Sai dai kuma, majiya ta bayyana cewa ana kan tattaunawa da masu garkuwa da mutanen da suka sace su

Kaduna - Yan uwan tsohuwar shugabar sashen injiniyan lantarki na makarantar kimiyya da fasaha ta Kaduna da aka sace, Injiniya Ramatu Abarshi, sun yi zargin cewa labaran da ke fitowa daga shafukan soshiyal midiya kan lamarin ya kusa jefa rayuwar ta da na diyarta a hatsari, Vanguard ta rahoto.

An yi zargin cewa yan bindigar sun nemi a biya naira miliyan 100 kudin fansar su.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Legit Hausa ta kawo a baya cewa yan bindiga sun sace injiniyar da diyarta a hanarsu ta komawa Kaduna bayan sun ziyarci wasu garuruwan kakkara domin raba masu kayan azumi da na Sallah karama.

Yadda rahotannin soshiyal midiya ya kusa jefa rayuwar Ramatu Abarshi da diyarta da aka sace a cikin hatsari
Yadda rahotannin soshiyal midiya ya kusa jefa rayuwar Ramatu Abarshi da diyarta da aka sace a cikin hatsari Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Daily trust ta rahoto cewa har yanzu yan bindiga na rike da injiniyar da diyarta da kuma direban da ya dauko su koda dai ana kan tattaunawa.

Wata majiya ta bayyana cewa:

“Yan bindiga sun yi garkuwa da su a kusa da Kasuwan Magani a karamar hukumar Kajuru, bayan sun kai kayan tallafi garin Mariri a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna a ranar 24 ga watan Afrilun 2022.
“Tana gudanar da gidauniyarta na taimakon talakawa mai suna 'Barkindo-Rahama Initiative' kuma tana yawan raba kayan amfanin gida ga talakawa da marayu, musamman gabannin bikin karamar sallah.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

“Har yanzu injiniyar da diyarta suna tsare a hannun yan bindiga koda dai muna kan tattaunawa har yanzu.
“Ba ma son yin sharhi kan lamarin saboda labarai daban-daban da aka rahoto a shafukan soshiyal midiya kan lamarin ya kusa jefa rayuwarsu a hatsari.”

Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m

A baya mun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai aikin taimakon jama’a, Ramatu Abarshi, da diyarta Amira, bayan sun gama raba kayan fitan sallah ga al’umman garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa yan bindigar sun farmake su ne a ranar Asabar da rana a kusa da Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kachia, a yankin kudancin Kaduna, Daily Nigerian ta rahoto.

Misis Abarshi, tsohuwar shugabar sashen Injiniyan Lantarki na kwalejin jihar Kaduna, ta yi suna sosai wajen aikin taimakon jama'a da shirin zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel