Mun Haɗa Baki Mu Yi Garkuwa Da Ɗan Majalisa Ne Domin Baya Taimakon Kowa, In Ji Waɗanda Ake Zargi

Mun Haɗa Baki Mu Yi Garkuwa Da Ɗan Majalisa Ne Domin Baya Taimakon Kowa, In Ji Waɗanda Ake Zargi

  • Wadanda su ka halarci wani bikin aure da aka yi a anguwar Uquo da ke karamar hukumar Esit Eket ta Jihar Akwa-Ibom ba za su taba mantawa da mummunan lamarin da ya faru ba a ranar 4 ga watan Nuwamban 2021 ba
  • Ana tsaka da shagalin biki, masu garkuwa da mutane su ka afka wurin inda su ka dinga harbe-harbe ta ko ina har su ka halaka mutane biyu yayin da su ka yi yunkurin sace wani dan majalisar jihar, Mr Usoro Samuel Akpanusoh
  • Sai dai ya ci babbar sa’a yayin da ya yi gaggawar tserewa zuwa motarsa, daga baya binciken ‘yan sanda ya nuna mutane 3 wadanda ke da alhakin shirya garkuwa da dan majalisar don tatsar kudade a wurinsa kafin zabe saboda a cewarsu ba ya taimako

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Akwa-Ibom - Wani mummunan lamarin ya faru a anguwar Uquo da ke karamar hukumar Esit Eket a cikin Jihar Akwa-Ibom a ranar 4 ga watan Nuwamban 2021, Vanguard ta ruwaito.

Ana tsaka da bikin aure sai masu garkuwa da mutane su ka bayyana da miyagun makamai su na ta harbi ko ta ina har su ka halaka mutane biyu take yanke.

Mun Haɗa Baki Mu Yi Garkuwa Da Ɗan Majalisa Ne Domin Baya Taimakon Kowa, In Ji Waɗanda Ake Zargi
Mun shirya garkuwa da dan majalisar Akwa-Ibom ne saboda ba ya taimakon kowa, wadanda ake zargi. Hoto: The Nation.

Yayin da mutane su ka dinga guduwa don neman tsira, akwai dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Esit Eket/Ibeno, Mr Usoro Samuel, wanda ya ke cikin manyan baki.

Yan sa kai na yankin ne da kuma wani jagoran matasa su ka shirya garkuwa da dan majalisar

Vanguard ta ruwaito cewa saboda shi aka kai farmakin, sai dai ya ci babbar sa’a inda ya yi saurin tserewa daga hannun daya daga cikin masu garkuwa da mutanen da ya kama shi zuwa motarsa.

Kara karanta wannan

Wani Bam ya ƙara tashi mutane na tsaka da holewa a jihar Kogi, rayuka sun salwanta

Bayan labari ya je wa Sifeta Janar na ‘yan sanda, IGP Alkali Usman Baba, ya yi hanzarin tura jami’an tsaro masu binciken sirri don gano masu alhakin shirya aika-aikar.

Bayan kwashe watanni biyar ana bincike, an kama mutane uku a cikin kungiyar ‘yan ta’addan da su kai harin yayin da har yanzu ake ci gaba da binciken.

Abin ban mamaki shi ne yadda daya daga cikinsu ya kasance wani jagoran matasan yankin wanda aka yi hayarsa don kula da dan majalisar a wurin bikin, yayin da sauran duk ‘yan kungiyar sa kai ne.

Cikin wadanda aka kama akwai Emmanuel Okon Johnny, Effiong Okon da Kingsley Emmanuel, kuma sun bayyana cewa sun yi shirin garkuwa da dan majalisar ne don samun makudan kudade daga hannunsa kafin zabe.

Yadda su ka yi shirin

Sun bayyana cewa sun yi shirin ne musamman don satar dan majalisar amma kashe-kashen sam ba ya cikin tsarinsu.

Kara karanta wannan

Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5

Johnny mai shekaru 29, wanda ya ce shi dan kungiyar matasan garin Uquo ne ya ce aikin da aka ba shi shi ne tabbatar da zuwan dan majalisar.

Daya daga cikinsu ya ce:

“A matsayina na daya daga cikin mambobin kungiyar matasa, na san yallabai kwarai kuma ya san ni dakyau. Wani fitaccen mai garkuwa da mutane ya shirya mana yadda za mu yi garkuwa da dan majalisar.
“Na amince da shiga shirin ne saboda da zarar za a fara kamfen don zabe sai dan majalisar ya rarraba mana kudade don mu zabe shi. Amma idan zabe ya wuce sai ya share mu ya koma kan iyalansa.
“Matasa ba su taba amfana da shi ba kuma bai taba yi wa garin mu wani abin kirki ba. ‘Yan uwansa kadai ya samar wa ayyuka da kuma na kusa da shi.”

Ya ce da an samu nasara da yanzu an ba shi N5m don ya fara kasuwanci

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Sauya Ra'ayinsa Kan Tikitin APC, Ya Nuna Alamun Zai Amince Ya Yi Takarar

Ya ci gaba da bayyana yadda su ka fara kai farmakin yayin da dan majalisar ya tashi zai shiga mota, daga nan ya yi gaggawar shiga motar ya tsere yayin da matasa biyu su ka halaka.

Ya ce yayin da Uyime da sauran mambobin kungiyar su ka tsere da bindigarsu, ya shiga cikin matasa su na kokarin koma masu garkuwa da mutanen.

A cewarsa, bai san yadda aka yi ‘yan sanda su ka gano yana da hannun a harin ba, kuma yanzu haka yana ta taimakon hukuma don neman su Uyime amma har yanzu babu labarinsu.

Ya ci gaba da cewa da an yi nasarar garkuwar da yanzu ya samu naira miliyan 5 wacce ya yi shirin fara kasuwanci da ita.

Kuma ya shiga harkar ne saboda dan siyasar ba ya taimako ko kadan amma ba su yi shirin halaka kowa ba.

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur

Kara karanta wannan

An kuma, Bam ya tashi a kusa da sansanin Sojojin Najeriya a babban birnin jihar Arewa

A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.

Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.

An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164