Zamfara: Hoton Hatsabibin Shugaban Haramtaciyyar Ƙungiya Da Ƴan Sanda Suka Kama Saboda Kisar Gilla
- Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta bayyana yadda ta kama shugaban wata kungiyar ta’addanci, “Yansakai” a Jihar Zamfara
- Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya shaida, sun kama shi ne bayan ya jagoranci kai farmaki kauyen Tungar Dutsi
- A cewar kakakin, ‘yan kungiyar sun kai harin ne inda su ka dinga harbe-harbe ko ta ina har su na raunana jama’a yayin da su ka halaka mutum daya
Jihar Zamfara - Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta yi ram da shugaban wata kungiyar ‘yan ta’adda da ta addabi jama’a a jihar, 'Yansakai', Channels TV ta ruwaito.
Kakakin rundunar, Mohammed Shehu ya saki wata takarda wacce ta tabbatar da harin inda ya ce kamen na da alaka da addabar kauyen Tungar Dutsi da ke karkashin karamar hukumar Bukkuyum da kungiyar ta yi.
Har halaka wani mutum daya su ka yi
Kamar yadda takardar ta zo:
“A ranar 3 ga watan Mayun 2022, ofishin ‘yan sanda da ke Bukkuyum ya samu rahoto daga garin Tungar Dutsi da ke Gana a karamar hukumar Bukkuyum. An samu bayani akan yadda wata kungiyar ‘yan ta’adda wacce aka fi sani da 'Yansakai'daga kauyen Tungar Bido ta afka kauyen Tungar Dutsi bisa jagorancin shugaban kungiyar, Bala Minista.
“Sun isa kauyen ne da miyagun makamai kamar bindigogi duk da sunan shagalin sallah inda su ka dinga harbe-harbe ta ko ina, hakan ya daga hankalin jama’a.”
“Yayin da mutane su ka fara kalubalantarsu, sai su ka far musu da wukake da sauran makamai. Dalilin haka su ka halaka wani Surajo Alhaji Ali, mai shekaru 40.”
Ana ci gaba da bincike don gano su
Takardar ta nuna yadda ‘yan sanda su ka kama shugaban kungiyar yayin da sauran su ka tsere. Bayan an titsiye shi ya bayyana sunayen sauran ‘yan kungiyar.
Ana ci gaba da bincike don gano sauran wadanda su ka hada kai wurin yin aika-aikar don a yanke musu hukuncin da ya dace da su.
Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep
A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.
Asali: Legit.ng