'Barawo Ya Afka Fadar Sarki a Ogbomoso, Ya Zubarwa Wani Basarake a Fada Haƙora Biyu

'Barawo Ya Afka Fadar Sarki a Ogbomoso, Ya Zubarwa Wani Basarake a Fada Haƙora Biyu

  • Wani da ake zargin barawo ne ya kai farmaki fadar Soun na kasar Ogbomoso da niyyar satar tsadaddun abubuwa a fadar
  • Ana zargin miyagun kwayoyi ya sha ko kuma yana fama da matsalar tabin hankali inda ya afka wa daya daga cikin sarakan fadar
  • Bincike ya bayyana cewa sai da barawon ya cizge wa basaraken hakora biyu yayin da basaraken ya ke kokarin kwatar kansa daga hannunsa

Ogbomoso, Oyo - Wani barawo ya afka fadar Soun din kasar Ogbomoso a jihar Oyo kuma ana zargin satar kambu ko kuma wasu tsadaddun abubuwa ya je yi fadar, Vanguard ta ruwaito.

Majiya daga fadar ta sanar da Vanguard cewa barawon ya afka fadar ne bayan ya yi shaye-shaye ko kuma wata cutar tabin hankali ke damunsa, daga nan ya kai wa wani basarake, Aremole ba kasar Ogbomoso farmaki, Chief Sheu Ayinla.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

'Barawo Ya Afka Fadar Sarki a Ogbomoso, Ya Zubar Wa Wani Bafade Hakora Biyu
'Barawo Ya Afka Fadar Sarki a Ogbomoso, Ya Zubar Wa Wani Bafade Hakora Biyu. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya cire wa wani basarake hakora biyu

Bayan bincike, an gano cewa sai da ya cizge wa Chief Ayinla hakora biyu yayin da ya ke kokarin ganin ya kwace kansa daga hannun barawon.

Wani ganau ya shaida wa Vanguard cewa barawon ya dinga cewa, “Ina so in zama sabon sarki. Ina so a nada ni kujerar Soun din kasar Ogbomoso nan ba da jimawa ba.”

Wata majiya daga fada ta bayyana cewa mutumin ya dinga cewa shi ne sabon Oba, a ba shi kambun sarauta, babu wani Oba sai shi. Yana so ya zama sabon Oba. Daga nan ta fasa kwalbar tagogin fada da hannunsa amma karafan da ke kofofin sun hana shi shiga fadar. Sai ya koma ta baya inda nan ma ya kasa shiga.

Yayin tabbatar da shiga fadar, basaraken da aka cire wa hakora, Chief Ayinla, ya ce ya na zuwa fada kullum ne don tabbatar da komai ya na tafiya daidai, Naija Dailies ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Yayin dakatar da barawon daga shiga fadar ne ya kai wa basaraken farmaki

Ya ci gaba da cewa:

“Na je fada inda na kira mai sayar da abinci daga nan naga wani mutum ya shiga harabar fadar. Na bukaci sanin dalili inda ya kamo ni ya hau nushi na a fuska. Anan ya cire min hakora biyu.”

A bangaren sakataren fadar, Mr. Toyin Ajamu, ya ce babu kambun da barawon zai sata a fadar.

A cewarsa:

“Maganar gaskiya babu kambu a fadar Soun din Ogbomoso kuma barawon ya lalata kofar shiga harabar fadar da kuma asalin ta fadar.
“Mu na masu shawartar jama’a da su share duk wata jita-jitar da ke yawo akan cewa an sace kambun sarauta ko kuma wani abin daban. Duk ba gaskiya ba ne.”

Wani Da Ke Sallah a Masallacin Da Na Ke Limanci Ya Ɗirka Wa Matata Ciki, Liman Ya Faɗa Wa Kotu

A wani labarin, Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a Oyo ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ɗirka wa matarsa ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ƴaƴa uku da bai da tabbas nasa ne, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel