Ba zan sa a sake Kanu ba: Buhari ya yi watsi da bukatar shugabannin Igbo
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da bukatar shugabannin Igbo kan batun sakin Nnamdi Kanu
- A yau ne shugaban ya gana da shugabannin yankin Kudu, inda suka bijiro da batutuwa da suka shafi yankin ciki har da na Kanu
- Shugaba Buhari ya ce kamata ya yi a bar kotu ta bayyana adalcinta kan Nnamdi Kanu domin ganin yadda za ta kaya
Ebonyi - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a ya yi kira ga shugabannin Kudu-maso-Gabas da su kyale shari’ar da ake yi a kotu ta shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu a kasar.
Buhari ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin yankin Kudu maso Gabas da suka hada da shugabannin kungiyar Ohanaeze Ndigbo a sabon gidan gwamnati da ke Abakaliki, Vanguard ta ruwaito.
'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya
Shugaban wanda ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar a yau Juma'a, ya yi nuni da cewa matakin da kotu ta dauka kan lamarin Kanu shi za a bi.
Buhari ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake ta fama da matsalar rashin tsaro a kasar, inda ya ce duk wanda da aka gani dauke da bindigar AK 47 a kowane yanki na kasar nan, to a yi masa kallon dan ta'adda matukar ba jami'in tsaro bane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A bangare gudam ya kuma yabawa Gwamna David Umahi bisa ayyukan canza rayuwa da gwamnatin sa (Umahi) ta aiwatar, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Ka saki Nnamdi Kanu: Shugabannin Igbo sun kalli Buhari ido da ido, sun roki alfarma
A wani labarin, shugabannin yankin Kudu maso Gabas sun bukaci da a gaggauta sakin shugaban tsagerun IPOB, Nnamdi Kanu daga tsare shi da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi.
Shugabannin sun yi wannan roko ne a wata tattaunawa da suka yi da Buhari a zauren majalisar zartarwa da ke gidan gwamnati a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, inji rahoton Punch.
Buhari ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Ebonyi, kamar yadda rahotanni daga fadar shugaban kasa da gwamnatin Ebonyi ta bayyana, The Nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng