Da duminsa: Shugaba Buhari ya bada umurnin bude bodar Jibiya da wasu guda 3

Da duminsa: Shugaba Buhari ya bada umurnin bude bodar Jibiya da wasu guda 3

  • Bayan shekaru uku, shugaban kasa ya bada umurnin bude iyakar Najeriya dake Jibiya, jihar Katsina
  • Wannan na cikin jerin iyakoki hudu da aka bada daman budewa bayan hudun farko da aka bude a baya
  • A 2019, Shugaba Buhari ya rufe dukkan iyakokin kasa don dakile shigo da makamai da shinkafa

Hukumar kwastam ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin bude karin iyakoki guda hudu.

Iyakokin sun hada da Idiroko dake Ogun, Jibiya dake Katsina, Kamba dake Kebbi da Ikom dake Cross River.

Hukumar ya bayyana haka a sanarwa mai dauke da ranar wata 22 ga Afrilu, 2022 da E.I. Edorhe, mataimakin kwantrolan kwastam ya rattafa hannu, rahoton TheCable.

A cewar sanarwar:

"Sakamakon umurnin da shugaban kasa ya bada ranar 16 ga Disamba, 2020, na bude iyakokin; Mfum, Seme, Illela da Maigatari, an umurceni in sanar da ku cewa an sake bada umurnin bude wasu guda hudu; Idiroko, jihar state (kudu maso yamma); Jibiya, Katsina (Arewa maso yamma); Kamba, jihar Kebbi (Arewa maso yamma); da Ikom, Cross River (kudu maso kudu),”

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori tsohon kakakin majalisa Dogara daga majalisar wakilai

"Saboda haka, dukkan rundunonin Kwastam dake wajen su bi wannan umurni kuma su mayar da hankali."

Border
Da duminsa: Shugaba Buhari ya bada umurnin bude bodar Jibiya da wasu guda 3
Asali: Twitter

Za ku tuna cewa a Agustan 2019, Shugaba Buhari ya rufe dukkan iyakokin kasa don dakile shigo da makamai da shinkafa daga kasashen Afrikan dake makwabtaka da Najeriya.

A 2020, bisa shawaran ministar kudi, shugaban kasa ya sassauta yace a bude na Seme, llela, Maigatari da Mfum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel