Hajjin bana: Kano ta baiwa maniyyata wa’adin kwanaki 7 su cika kudinsu
- Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano ta baiwa masu niyan sauke farali na wannan shekarar wa'adin kwanaki bakwai su cika kudinsu
- KSPWB ta kara yin tuni ga cewar an haramtawa tsoffin da shekarunsu ya haura 65 zuwa aikin hajji a bana
- Sai dai kuma ta bayyana cewa za ta baiwa wadanda suka fara ajiyar kudadensu a hannun hukumar fifiko
Kano - Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano (KSPWB) ta baiwa maniyyata zuwa hajji wa’adin kwanaki bakwai domin su kammala biyan kudinsu.
Babban sakataren hukumar, Alhaji Mohammad Abba Danbatta, ya bayar da wa’adin ne yayin da yake zantawa da manema labarai kan shirye-shiryen hajjin 2022, a ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Danbatta ya kuma tunatar da wadanda ke sama da shekaru 65 cewa an haramta masu zuwa aikin Hajji a bana, rahoton Kano Focus.
Hukumar aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa ana tsammanin biyan naira miliyan 2.5 a matsayin kudin kujerar Hajji na shekarar 2022 zuwa lokacin da za a fitar da jadawalin karshe na farashin da kowace jiha za ta biya.
Ya ce:
“Hukumar aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta kuma bayar da Naira miliyan 2.5 a matsayin farashin kudin gudanar da aikin na shekarar 2022 sakamakon tashin farashin dala da kuma karin kudaden haraji daga Saudiyya da kamfanin jiragen sama.
“Hukumar tana da akalla mutane 2,500 da suka bayar da wani kaso na kudaden aikin Hajji kuma za su ba da fifiko ga wadanda suka fara ajiye kudadensu ga hukumar.”
Aikin Hajji zai tashi a shekarar bana, kudin sauke farali zai karu da fiye da 50% inji NAHCON
A wani labarin kuma, ukumar nan ta National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) mai kula da aikin Hajji a Najeriya ta ce kudin aikin wannan shekarar zai karu.
Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban hukumar NAHCON na kasa, Zikrullah Hassan yana cewa hasashensu ya nuna kudin kujera zai karu da akalla 50%.
Abin da mahajatta suka biya a shekarar 2019 ya kai N1.5m. maganar da ake yi a bana, duk wadanda suka bada kudi tun 2020 sai sun cika akalla N1m.
Asali: Legit.ng