Kyawawan hotunan sarauniya Firdaus Bayero yayin da Oluwo na Iwo, angonta ya bata kambu
- Oluwo na Iwo, Oba Abdulrashid Adewale Akanbi ya sake assasa soyayyar da yake wa sabuwar amaryarsa Firdaus zuwa matakin gaba
- Basaraken ya wallafa hotunansu a shafinsa yayin da ya sanar da nada sabuwar amaryarsa matsayin sarauniyarsa saboda irin kaunar da yake ma ta
- Sarkin ya kasa boye irin kaunar da yake wa Firdaus Bayero, hakan ya bayyana a hotunan da ya wallafa na santaleliyar sarauniyar a fadarsa
An nada sabuwar amaryar Oluwo na Iwo, Oba Abdulrashid Adewale Akanbi Firdaus, a matsayin sarauniyar fadarsa.
Basaraken ya sanar da hakan ne a shafinsa na Instagram tare da wallafa zankada-zankadan hotunansu tare da nuna kauna ga tsaleliyar gimbiyar da aka haifa a jihar Kano.

Asali: Instagram
Yayin bayyana dalilin nada sarauniyarsa, Oluwo ya ce duk wata sarauniya ra cancanci a bata kambu, kuma yana matukar kaunar tasa sarauniyar.

Kara karanta wannan
Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu
Ya kara da cewa, ya bi koyarwan magabatansa ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Madaukakin kakana Oduduwa ne ya koyar da ni kaunar sarauniyata ta hanyar bata kambu, shiyasa na ba wa Olokun, matata," yace.
Jama'a sun yi tsokaci
Tsokacin jama'a:
Alase Lori Orisa "Duk don sarauniya Firdaus, gaskiya wannan 'yar gata ce!!!"
jayeola_monye: "Santaleliyar sarauniya;."
opetodolapo: "Ya Ubangijina!!! Irin wannan kyau haka, tabbas akwai sarauta a jininta. An albarkace ki da Kabiyesi!
iambolsjitlawal: "Wannan irin zankadediyar sarauniya."
olamiaduks: "Da izinin Allah wannan aure ne na har abada"
akintaro_dahood: "Olorinmu, muna alfahari dake."
claragold082: "Zankadediyar Oloti Kabiyesi oooo Barka da sallah."
Hotunan matar basaraken Yarabawa da ta karba Musulunci, ta koma Khadija daga Joyce
A wani labari na daban, sarauniya Joyce Anene Balogun, matar basarake Olubadan na kasar Ibadan, Oba Lekan Moshood Balogun, ta karba kalmar shahada.

Kara karanta wannan
Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi
Sarauniyar ta karba kalmar shahada ne inda ta koma addinin Musulunci a wani wa'azin watan Ramadan da aka yi a ranar Litinin, 25 ga watan Afirilu a babban filin sallah na Ibadan karkashin shugabancin Honarabul Ibraheem Akintayo.
Babban limamin jihar Oyo, Sheikh Abdul Ganiyy Abubakary Agbotomokekere I, ya tabbatar da hakan a wallafar da yayi a shafinsa na Facebook inda ya kara da cewa sabon sunan sarauniyar shi ne Khadijah Mashood Lekan.
Asali: Legit.ng