Sarkin Kano: Kowa ya tanadi katin zabensa na dindindin kafin zaben 2023
- Yayin da zaben 2023 ke gabatowa, Sarkin Kano ya shawarci jama'a da su tanadi katin kada zabe na dindindin kafin lokacin zabe
- Ya kuma bayyana bukatar jama'a su zauna lafiya tare da lura da 'ya'yansu ganin yadda siyasa ke kara karatowa
- Gwamnan Kano, shi ma ya fadi albarkacin bakinsa dangane da ci gaban jihar da kuma irin ayyukan da gwamnatinsa ke yi
Kano - Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya bukaci masu kada kuri’a da su karbi katin zabe na dindindin (PVC) a shirye-shiryen tunkarar zaben 2023 mai zuwa.
Sarkin Bayero ya yi wannan kiran ne a jiya yayin bikin gargajiya na Hawan Nasarawa a gidan gwamnati da ke Kano, Daily Trust ta ruwaito.
NAN ta ruwaito cewa Hawan Nasarawa biki ne na karramawar da sarkin ya yiwa gwamnan jihar bayan kammala bukukuwan Sallah.
Sarkin ya kuma shawarci matasan jihar da su nisanci aikin barna, musamman shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula
Hakazalika ya roki iyaye da su sanya ido kan motsi da ayyukan ‘ya’yansu domin gujewa duk wata damuwa.
Ya yi tir da barazanar ‘yan daba a jihar tare da yin kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da sa ido.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da zama lafiya da juna ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.
A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Ganduje ya godewa sarkin bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a jihar.
Ya kuma danganta zaman lafiya da ake samu a jihar sakamakon daukar sabbin matakan tsaro, aikin sa kai na al’umma da inganta hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro, inji rahoton The Nation.
Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ta dauki dabarun kara inganta kasuwanni ta hanyar samar da yanayin da zai sa ‘yan kasuwa su ci gaba.
Dangane da matsalar karancin ruwa da ake fama da shi a wasu sassan birnin Kano, Ganduje ya ce ayyukan gyara da fadada ayyukan da gwamnatin tarayya ta fara a wasu yankunan ya hada da samar da ruwan sha a babban birnin jihar.
Kano: An Kama Shugabannin PDP Kan Lalata Komfutoci Da Tarwatsa Taron Ɗayan Ɓangaren Shugabannin Jam'iyyarsu
A wani labarin, wasu mambobin jam’iyyar PDP a Jihar Kano na bangaren Shehu Sagagi su na hannun ‘yan sanda bayan sun lalata taron shugabannin dayan bangaren jam’iyyar da aka yi a Tahir Hotel da ke Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.
Cikin wadanda aka kama akwai ma’ajin jihar, Idi Zare Rogo; Sakataren harkokin kudin jihar, Dahiru Arrow Dakara; Shugaban matasan jihar, Hafizu Bunkure da kuma shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Kumbotso, Idi Mariri.
Har yanzu ‘yan sanda ba su riga sun saki takarda ba akan lamarin, amma majiya daga jami’an tsaro ta bayyana yadda yanzu haka su ke hedkwata da ke Bompai su na amsa tambayoyi akan lamarin.
Asali: Legit.ng