Kano: An Kama Shugabannin PDP Kan Lalata Komfutoci Da Tarwatsa Taron Ɗayan Ɓangaren Shugabannin Jam'iyyarsu

Kano: An Kama Shugabannin PDP Kan Lalata Komfutoci Da Tarwatsa Taron Ɗayan Ɓangaren Shugabannin Jam'iyyarsu

  • Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano ta kama wasu ‘yan PDP na bangaren Shehu Sagagi bayan sun rushe taron shugabannin jam’iyyar na dayan bangaren
  • An yi taron ne a Tahir Hotel ne, kuma cikin wadanda aka kama akwai ma’ajin jihar, sakataren harkokin kudi, shugaban matasan jihar da kuma shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Kumbotso
  • Duk da dai har yanzu ‘yan sanda ba su riga sun fitar da takarda ba, amma an samu labarin yadda yanzu haka su ke hedkwatar da ke Bompai su na amsa tambayoyi akan lamarin

Kano - Wasu mambobin jam’iyyar PDP a Jihar Kano na bangaren Shehu Sagagi su na hannun ‘yan sanda bayan sun lalata taron shugabannin dayan bangaren jam’iyyar da aka yi a Tahir Hotel da ke Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Cikin wadanda aka kama akwai ma’ajin jihar, Idi Zare Rogo; Sakataren harkokin kudin jihar, Dahiru Arrow Dakara; Shugaban matasan jihar, Hafizu Bunkure da kuma shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Kumbotso, Idi Mariri.

Kano: An Kama Shugabannin PDP Kan Lalata Komfutoci Da Tarwatsa Taron Ɗayan Ɓangaren Shugabannin Jam'iyyarsu
An Kama Shugabannin PDP a Kano Kan Lalata Komfutoci Da Tarwatsa Taron Ɗayan Ɓangaren Shugabannin Jam'iyyarsu. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Har yanzu ‘yan sanda ba su riga sun saki takarda ba akan lamarin, amma majiya daga jami’an tsaro ta bayyana yadda yanzu haka su ke hedkwata da ke Bompai su na amsa tambayoyi akan lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Nigerian ta tattaro yadda mambobin su ka afka otal din wanda ya ke cike da ‘yan jam’iyyar na bangaren Aminu Wali, su ka rusa taron nasu, su ka lakada wa wasu mambobi dukan-tsiya tare da yashe dakin tas inda su ka tsere da takardu da komfutoci.

Sun yi zargin ana taron ne don rubuta sunayen wakilan jam’iyya kafin ranar gangaminta na kasa

Kara karanta wannan

An yi ram da mai mulki a Kaduna yana dauke da AK-47 kusa da sansanin ‘Yan bindiga

Wata majiya ta bayyana cewa:

“Yayin da su ke zargin ana rubuta sunayen wakilan jam’iyyar ne kafin gangamin gaba daya jihar, sun afka dakin inda su ka rushe taron.”

Kwamitin Ayyuka ta Kasa ta jam’iyyar PDP ta dage gangamin jam’iyyar don zaben wakilin karamar hukuma daya zuwa ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu na kasa.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel