Gwamnan Kudancin Najeriya ya ci burin hana bara a titi, zai dauki tsattsauran mataki

Gwamnan Kudancin Najeriya ya ci burin hana bara a titi, zai dauki tsattsauran mataki

  • Nan da ‘yan kwanaki kadan ne za a ji Gwamnatin jihar Edo ta sa kafar wando daya da mabarata
  • Gwamna Godwin Obaseki ya sanar da hakan a lokacin da Musulmai su ka je yi masa yawon sallah
  • Babban limamin garin Benin, Alhaji Abdulfatai Enabulele ne ya yi kira ga gwamnan ya hana yin bara

Edo - Gwamnatin jihar Edo ta ce za ta fara dauke mabarata daga kan titi idan har ba za su nemi sana’ar kwarai, su samu hanyar ci daga guminsu ba.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, ta ce Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana wannan a lokacin da ya gana da Musulmai a Benin.

Kamar yadda mu ka samu labari, Musulmai sun kai wa Mai girma gwamnan ziyarar bikin sallah ne a gidan gwamnati da ke garin Benin a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Godwin Obaseki ya ja-kunnen al’umma da cewa za a fara kama iyayen yaran da aka samu a kan titi su na bara a jihar Edo, a maimakon su je makaranta.

Gwamnan ya ce za a kama iyayen yaran da suka saba wannan doka, kuma a gurfanar da su a kotu.

A cewar Gwamna Obaseki, nan da ‘yan kwanaki kadan zuwa wasu ‘yan watanni, ba za a cigaba da kyale mutane su rika yin bara a kan titunan Edo ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu mabarata
Wasu mabarata a Najeriya Hoto: www.dw.com
Asali: UGC

Za a kai mabarata gona

Jaridar ta rahoto Obaseki yana mai cewa duk wanda aka samu yana bara a bainar jama’a, za a kama shi, a kai shi gonaki domin ya yi aiki da karfinsa.

“Akwai filayen noma da yawa, kuma ana bukatar karin hannu domin a noma gonakin.”

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

- Godwin Obaseki

Idan kuma mabaratan ba su da niyyar ci da guminsu, Obaseki ya ce za a maida su inda suka fito. Asali da-dama daga cikin mabaratan ba ‘yan gari ba.

Gwamna Obaseki ya yi magana a game da sha’anin ilmi, ya ce gwamnatinsa ta dauki malamai 3, 062 aiki a makarantun kauyuka domin a bunkasa ilmi.

Kokarin kawo karshen matsalar

Babban limamin garin Benin, Alhaji Abdulfatai Enabulele ya yabawa gwamnatin PDP, tun farko shi ne ya bukaci a magance matsalar barace-barace.

A baya an samu wasu gwamnatoci da suka yi kokarin sa kafar wando daya da harkar bara a Najeriya. Har yanzu ana cigaba da fama da matsalar.

Hawan sallah a Zaria

An samu rahoto Mai martaba Sarkin Zazau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya dakatar da wasu Hakimai saboda amfani da 'yan daba wajen hawan sallah.

Masarautar Zazzau ta bakin Abdullahi Aliyu Kwarbai ta bada wannan sanarwa bayan an yi bikin idi. Kwarbai ya ce an hana amfani da 'yan daba a tawaga.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel