Karin haske: Tsohon shugaban APC ya bayyana aniyarsa ta gaje kujerar Buhari

Karin haske: Tsohon shugaban APC ya bayyana aniyarsa ta gaje kujerar Buhari

  • Adams Oshiomole, daya daga cikin jiga-jigan APC kuma tsohon gwamnan Edo ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa
  • Omshiomole dai na daga cikin wadanda ake ta zuba ido da yada jita-jitar zai tsaya takara, yanzu dai batu ya tabbata
  • Ya bayyana haka ne a Abuja, kuma zai tsaya takara ne a APC inda zai yi gogayya da su Tinubu da Osinbajo

Abuja - A ranar Laraba ne tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa Adams Oshiomhole ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, The Nation ta ruwaito.

Da yake bayyana aniyarsa a cibiyar fasaha da al’adu ta Cyprian Ekwensi Abuja, tsohon gwamnan na Edo ya ce ya shiga jerin wadanda za su fafata ne don canza kanun labarai ga daukacin ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Adams Oshiomole ya bayyana aniyar gaje Buhari
Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban APC ya bayyana aniyarsa ta gaje kujerar Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Oshiomole ya bayyana aniyarsa ne jim kadan bayan da ya karyata jita-jitar yana da sha'awar tsayawa takara a zaben 2023.

Ya zuwa yanzu dai jiga-jigai daga APC na ci gaba da nuna sha'awarsu ga dane kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wacce hawanta ya nuna sai mai sa'a.

Buhari yana sauka zan dane kujerarsa

Oshiomhole ya ce ba wai ya tsaya takara ne don kokawa da jimamin kura-kuran baya a kasar nan ba, zai yi takara ne ne domin dora Najeriya a kan turbar ta gari da daukaka, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Ya jaddada cewa bisa ka’idojin tsarin mulkin kasar nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar ofishin a ranar 29 ga Mayu, 2023, don haka ya yanke shawarar maye gurbinsa a matsayin shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

Oshiomhole ya lura cewa tattalin arzikin kasar nan ya kasance babban maudu'in magana, duk da kokarin da gwamnatin APC ta yi kuma take yi na habaka shi.

2023: 'Yan APC a yankin Yarbawa za su zauna, su hada kai su zabi mai gaje Buhari daga yankinsu

A wani labarin na daban, shugabanin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso Yamma za su gana da masu neman takarar shugaban kasa na yankin a ranar Juma’a a jihar Legas, kamar yadda jaridar WesternPost ta ruwaito.

An bayyana cewa taron zai gudana ne a gidan gwamnatin Legas.

Rahoton da Legit.ng Hausa ke samu daga TheCable ya bayyana cewa Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC ne zai jagoranci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.