Labari mara dadi: 'Yan ta'addan ISWAP na can suna barna a garin Chibok, sun kori sojoji

Labari mara dadi: 'Yan ta'addan ISWAP na can suna barna a garin Chibok, sun kori sojoji

  • Labarin da ke iso mu ya bayyana cewa, yanzu haka 'yan ta'addan ISWAP na can na barna a wani yankin Borno
  • Rahotanni sun bayyana cewa, mayakan sun farmaki sojoi tare da fatattakarsu a wani sansani da ke yankin
  • Mazauna yankin ance sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu yayin da 'yan ta'addan ke barna

Borno - Kautukari da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno a halin yanzu na fuskantar harI daga wasu da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP.

Wani mazaunin garin ya shaidawa TheCable cewa ‘yan ta’addan sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata inda suka fara harbe-harbe ba kakkautawa.

Rahotanni sun ce mayakan na ISWAP sun kona gidaje yayin da mazauna yankin ke tserewa cikin daji domin tsira da rayukansu.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

'Yan ta'adda sun kai hari Chibok
Labari mara dadi: 'Yan ta'adda sun kai hari a garin Chibok, sun kori sojoji | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An ce 'yan ta'addan sun kori sojojin da ke wani sansanin soji na FOB da ke Kada mai tazarar kilomita biyu daga Kautukari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai majiya ta fahimci cewa an tattara sojoji daga bataliya ta 117 da ke garin Chibok zuwa yankin.

Kautukari dai na da tazarar kilomita 17 ne daga garin Chibok.

Kokarin samun Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin kasar, domin jin ta bakinsa kan lamarin bai samu ba.

Harin ya faru bayan ziyarar Antonio Guterres

Harin dai ya faru ne sa’o’i bayan da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kai ziyararsa ta farko a Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Guterres ya isa Maiduguri ne da yammacin ranar Talata a wani bangare na ziyarar aiki ta kwanaki 2 a Najeriya.

Ya gana da Gwamna Babagana Zulum, tubabbun mayakan Boko Haram da wadanda rikicin ta'addan yankin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Guterres, wanda tun da farko ya ziyarci Jamhuriyar Nijar, zai kammala ziyararsa ta watan Ramadan a nahiyar Afirka da ziyarar aiki a kasar Senegal.

Kano: An kama bazawara mai shekaru 30 da shiga harkallar miyagun kwayoyi

A wani labarin, rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wata bazawara mai shekaru 30 a duniya, Jamila Abdullahi, kan zargin har kar siyar da kwayoyi.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 2 ga watan Mayu, ya ce wacce ake zargin ta amsa cewa tana harkar siyar da kwayoyi sama da shekaru biyu, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Ya ce: “A ranar 30/03/2022 da misalin karfe 1200hrs, wasu bayanai abun dogaro da aka samu ya nuna cewa wata Jamila Abdullahi mai shekaru 30, ta Kwanar Ungogo Quarters, karamar hukumar Ungogo jihar Kano tana harkallar siya da siyar da miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.