Kano: An kama bazawara mai shekaru 30 da shiga harkallar miyagun kwayoyi

Kano: An kama bazawara mai shekaru 30 da shiga harkallar miyagun kwayoyi

  • Jami'an rundunar yan sanda a jihar Kano sun yi ram da wata bazawara mai suna Jamila Abdullahi
  • An kama Jamila wacce ke zama a Kwanar Ungogo ne kan zargin shiga harkallar miyagun kwayoyi
  • An taba kama matar wacce ita ce dilar ‘Rubber Solution’ a yankin inda ta saka hannu kan yarjejeniyar cewa ba za ta sake harkar ba amma kuma sai ta koma ruwa

Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wata bazawara mai shekaru 30 a duniya, Jamila Abdullahi, kan zargin har kar siyar da kwayoyi.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 2 ga watan Mayu, ya ce wacce ake zargin ta amsa cewa tana harkar siyar da kwayoyi sama da shekaru biyu, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Kara karanta wannan

Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

Kano: An kama bazawara mai shekaru 30 da shiga harkallar miyagun kwayoyi
Kano: An kama bazawara mai shekaru 30 da shiga harkallar miyagun kwayoyi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce:

“A ranar 30/03/2022 da misalin karfe 1200hrs, wasu bayanai abun dogaro da aka samu ya nuna cewa wata Jamila Abdullahi mai shekaru 30, ta Kwanar Ungogo Quarters, karamar hukumar Ungogo jihar Kano tana harkallar siya da siyar da miyagun kwayoyi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi ya umarci DPO na reshen Ungogo, SP Murtala Mohammed Fagam da ya gayyaci matar da ‘yan sanda na yankin. An gayyace ta kuma a gaban 'yan uwanta da mai unguwarsu ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da ba za ta sake shiga irin wannan aikin ba.
“A ranar 30/04/2022 da misalin karfe 1000, wata tawagar Operation Puff Adder karkashin jagorancin DPO na yankin Ungogo yayin da suke sintiri a unguwar Kwanar Ungogo, ta kama jamila, dauke da kwayoyin roba guda 35."

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Bayanai abun dogaro sun nuna cewa ita ce babbar dilar wannan kwayar ta ‘Rubber Solution’ a karamar hukumar Ungogo da kewaye.

Yayin bincike, Jamila ta tona cewa ita bazawara ce, kuma ta yi kimanin shekaru biyu tana sana’ar siye da siyar da kwayar. Bayan gayyatar farko da aka mata ta daina, amma daga baya ta koma harkar.

Ta ci gaba da cewa tana siyan kwayoyin daga wajen wani. Bayan samun labarin kama ta, an tattaro cewa mutumin ya tsere kuma ya bar kasar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi a sashin binciken manyan laifuka na rundunar, inda daga nan ne za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu.

NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol na 2.3m, 396Kg na Codeine a Kaduna

A wani labarin, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi ta jihar Kaduna (NDLEA) ta ce jami'anta sun kama kwayoyin tramadol na 2.3 miliyan a cikin jihar.

Kara karanta wannan

An yi ram da mai mulki a Kaduna yana dauke da AK-47 kusa da sansanin ‘Yan bindiga

Mai Jama'a Abdullahi, kakakin rundunar NDLEA ta Kaduna, ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, TheCable ta ruwaito.

A cewar Abdullah, kwayoyin sun kai nauyin 1.2 tonnes, sannan an kama maganin tari na codeine yayin da jami'an hukumar suka kai wani samame a ranar Litinin da Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel