An tsinta gawar magidanci da budurwa a mota, sun mutu suna tsaka da 'kece-raini'

An tsinta gawar magidanci da budurwa a mota, sun mutu suna tsaka da 'kece-raini'

  • An tsinta gawar wani magidanci tare da budurwarsa a cikin motarsa kirar SUV a Jakande da Isolo sun tsaka da 'kece-raini'
  • An gano cewa, magidancin mai suna Koyejo ya dauko budurwarsa kuma ya siya tsire kafin ya ajiye motar su fara jima'i
  • Hankalin mazauna yankin ya kai kansu ne bayan an ga motar a kunne tun daga Asabar har zuwa Lahadi, gawawwakinsu ta fara lalacewa

Legas - An tsinta gawar wani mutum da wata mata wadanda aka gano sun mutu a cikin mota kirar SUV yayin da suke tsaka da jima'i.

The Nation ta ruwaito cewa, an tsinta gawarsu a daren Lahadi a rukunin gidaje na Jakande da ke Isolo a jihar Legas yayin da makwabta da suka balle motar bayan sun lura da injinta a kunne tun daga ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

An tsinta gawar saurayi da budurwa a mota, sun mutu sun tsaka da 'kece-raini'
An tsinta gawar saurayi da budurwa a mota, sun mutu sun tsaka da 'kece-raini'. Hoto daga thenationonlinng.net
Asali: UGC

Mutumin mai suna Koyejo ya dauka masoyiyarsa wacce ba a san sunanta ba yayin da yake hanyarsa ta zuwa gidan iyayensa da ke rukunin gidaje na Jakande a Isolo kamar yadda abokansa suka yi ikirari.

Vanguard ta ruwaito cewa, ya siya tsire kafin ya tsayar da motarsa daidai Double Star domin ya dan shakata a cikin motar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Koyejo yana da mata kuma Injinya ne wanda bai dade da tashi daga rukunin gidaje na Jakande ba da ke Surulere tare da matarsa.

Wata majiya ta ce motar da aka gani a wuri daya da kuma injinta da ke kunne na tsawon kwana daya ne ya ja hankalinsu.

"A lokacin da mutane suka kunna fitilunsu, sun gane cewa Koyejo ne, tsohon makwabcinmu kuma abokinmu. Amma ba mu san budurwar da suke tare ba.
"Da yammacin nan ne aka sanar mana da cewa ya dauko budurwar ne daga Isolo. Sun siya tsire a tashar mota ta Moshalashi. Daga wani abu zuwa wani, a hankali suka zarce da jima'i a cikin mota," wani ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

"Daya daga cikin mutanen yankinmu ya kira matar Koyejo kuma ta tabbatar da cewa ta kasa samun Koyejo a waya tun ranar Asabar. Ko ta kira a kashe ta ke jin ta.
“Dole ta sa muka kira 'yan sanda da ke Ejigbo wadanda suka zo tare da dauke su a motar. Gawar Koyejo ta fara rubewa, ita kuma budurwar hancinta na fitar da jini," wata majiya tace.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace gwajin likitoci ne kadai zai iya tabbatar da abinda ya kashe su.

An kwantar da budurwa a asibiti bayan ta ƙunshe tusa tsawon shekara 2 saboda kunyar saurayi

A wani labari na daban, an garzaya da wata matashiyar budurwa, mai shekaru 19 asibiti bayan ta matse tusa a gaban saurayinta na tsawon shekaru biyu.

Shafin LIB ya ruwaito cewa, wata mata ta bada labarin yadda ta ƙare a asibiti, gami da buƙatar aikin gaggawa saboda yadda ta riƙe tusa a lokacin da take tare da saurayin ta na tsawon shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Wata mata mai sana'ar siyar da abinci da daɓa wa tsohon saurayinta wuƙa kan N500

Cara Clarke, mai shekaru 19, na wurin aiki lokacin da cikin ta ya fara "matsanancin ciwo" a ranar Talata, 29 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel