An kwantar da budurwa a asibiti bayan ta ƙunshe tusa tsawon shekara 2 saboda kunyar saurayi

An kwantar da budurwa a asibiti bayan ta ƙunshe tusa tsawon shekara 2 saboda kunyar saurayi

  • An garzaya da wata budurwa mai shekaru 19 bayan daukar tsawon lokaci tana matse tusa a gaban saurayinta
  • Hakan ya ja sai da aka ma ta aikin gaggawa a ranar Talata, 29 ga watan Maris, sannan ta kwashe kwanaki biyu tana jinya a asibiti
  • Cara Clarke, wacce lamarin ya auku da ita, ta lashi takobin ba za ta sake matse tusa ba, daga yanzu sakin abin ta za tayi da zarar ta ji

An garzaya da wata matashiyar budurwa, mai shekaru 19 asibiti bayan ta matse tusa a gaban saurayinta na tsawon shekaru biyu.

Shafin LIB ya ruwaito cewa, wata mata ta bada labarin yadda ta ƙare a asibiti, gami da buƙatar aikin gaggawa saboda yadda ta riƙe tusa a lokacin da take tare da saurayin ta na tsawon shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malaysia za ta daure ko cin tarar 'yan kasa da ke cin abinci da rana a Ramadan

An kwantar da budurwa a asibiti bayan ya ƙunshe tusa tsawon shekara 2 saboda kunyar saurayi
An kwantar da budurwa a asibiti bayan ya ƙunshe tusa tsawon shekara 2 saboda kunyar saurayi. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Cara Clarke, mai shekaru 19, na wurin aiki lokacin da cikin ta ya fara "matsanancin ciwo" a ranar Talata, 29 ga watan Maris.

An garzaya da ita asibiti, inda aka tabbatar da tana fama da cutar appendicitis, kamar yadda shafin LIB ya ruwaito.

Cara tayi imani da cewa, matse tusar da tayi tayi a gaban saurayinta, da takura wa kanta da tayi ne ya jafa ta a halin da ta tsinci kanta a ciki.

Barista da ta dauka shekaru biyu tare da saurayinta mai shekaru 21, Kyle Duffy, ta tuna yadda ya ci dariya bayan ya gano kokarin da take don ganin ba tayi tusa a gabanshi ba, wanda hakan ne ya sa ta bukatar a yi ma ta aiki.

Kara karanta wannan

Gabansa ba ya aiki: Tsohuwa mai shekaru 54 ta nemi saki a gaban kotu

Cara ta lashi takobin "sakin tusoshinta daga yanzu", bayan ta ce bata da masaniya a kan yadda riƙe tusa ke da hatsari ba.

Care, daga Louth, Ireland, ta ce: "Ina matse tusoshi na, amma a yanzu bana tunanin zan sake dawowa asibiti a kan haka.
"Bana da wata matsalar da ta wuce in yi ta sakin tusoshi na. Ina wajen aiki a ranar Talata, inda matsanancin ciwon ciki ya kamani.
"Na isa wurin likita, wanda ya ce in wuce asibiti kai tsaye. Na shiga cikin matsanancin azabar da na kasa riƙe hawayena.
"Likita na ya ce min ki yi hakuri kina fama da matsanancin ciwon ciki. Da kyar nake tafiya saboda azaba.
"Kyle ya sha dariya. Maganar gaskiya ya rasa me zai ce. Ya ce, Ubangiji, mutane za su yi tunanin kina tsoron yin komi tare dani.
"A wannan matakin, daga yanzu sakin tusoshina zan tayi da zarar na ji."

Kara karanta wannan

Bidiyon budurwar da ta dauka nauyin aurenta da saurayinta, sun rabu cikin kwanaki 120

Care ta bar asibitin bayan kwanaki biyu, a yammacin Alhamis, 31 ga watan Maris.

Ta ce: "Aikin ba babba bane, wanda zai dauki lokaci. An dora ni a kan magunguna masu kashe raɗadi, sannan an ce zan iya komawa aiki wani satin.
"A yanzu hutawa ta nake, gami da amfani da damar yadda kowa ke kula dani."

Bidiyon budurwar da ta dauka nauyin aurenta da saurayinta, sun rabu cikin kwanaki 120

A wani labari na daban, wata bazawara ta bayar da labarin yadda ta yi nadamar aure da darussan da ta koya bayan ta rabu da tsohon mijinta kuma masoyinta.

Matar mai suna June Katei Reeves 'yar asalin kasar Kenya ce wacce ta yi soyayya da tsohon mijinta na tsawo shekaru tara amma aurensu watanni hudu kacal ya yi sakamakon rashin zaman lafiyan da suke fuskanta.

A wata doguwar tattaunawa da aka yi da Lynn Ngugi, matar 'yar asalin kasar Kenya ta ce duk da ta yi aure, ita ce ta dauka nauyin dawainiya da gidan da kuma mijinta mai jini a jika. Mijinta ba ya kawo komai gidan.

Kara karanta wannan

Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel