Eid-El-Fitr: Shugaba Buhari ya ce ba ya iya runtsawa da daddare saboda rashin tsaro a Najeriya

Eid-El-Fitr: Shugaba Buhari ya ce ba ya iya runtsawa da daddare saboda rashin tsaro a Najeriya

  • Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ko kaɗan ba ya iya kwantawa ya yi bacci saboda matsalar tsaron da ta dami Najeriya
  • Jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi a Barikin Mambila, Buhari ya ce ba zai raga wa yan ta'adda ba har sai ya ga bayan su
  • Ya kuma tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatinsa zata tabbatar da an yi ingantacce kuma sahihin zaɓe a 2023

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya haɗu da sauran yan uwa musulmai a filin Fareti na Barikin sojojin Mambila domin gudanar da Sallar Eid-El-Fitr wato ƙaramar Sallah.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa shugaban kasan, tare da wasu daga cikin iyalansa da hadimansa sun isa wurin Idi da misalin ƙarfe 9:00 na safiya.

Sauran mutanen da suka halarci Masallacin idin sun haɗa da mambobin majalisar zartarwa, hafsoshin tsaro, shugabannin hukumomin tsaro da wasu jiga-jigan gwamnati, Premium times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Shugaban ƙasa Buhari a Masallacin Idi.
Eid-El-Fitr: Shugaba Buhari ya ce ba ya iya runtsawa da daddare saboda rashin tsaro a Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An gudanar da Sallar Idi mai Raka'a biyu bisa jagorancin Limamin Barikin, Muhammad Dahey-Shuwa, wanda ya yi nasiha kan muhimmanci da darussan watan da ya gabata wato Ramadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A huɗubar da limamin ya gabatar, ya yi addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan, inda ya bukaci mutane su cigaba da kai kukansu ga Allah kuma su taimaka wa jami'an tsaro.

Jawabin Buhari bayan kammala Sallah

Yayin amsa tambayoyi bayan kammala ibadar Sallah Eid, Buhari ya ce baya iya bacci da dare saboda rashin tsaron da ake fama da shi a wasu sassan ƙasar nan.

Ya kuma yi alƙawarin cewar ba zai gajiya ba wajen jajircewa a kokarin kawo ƙarshen dukkan ƙungiyoyin yan ta'adda.

Dangane da zaɓen 2023 dake tafe, Buhari ya ƙara jaddada shirin gwamnatinsa na tabbatar da an gudanar da ingantace kuma sahihin zaɓe babu ɓoye-ɓoye.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

A gaba ɗaya watan Azumin Ramadana, Shugaba Buhari ya kasance yana halartar Masallacin fadar shugaban kasa wajen Tafsirin Alƙur'ani mai girma.

A wani labarin kuma A Ranar Ma'aikata, wani Gwamna a Najeriya ya ƙara mafi karancin Albashi zuwa N40,000

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙara mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiharsa daga N30,000 da gwamnatin tarayya ta ƙayyade zuwa N40,000.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana wannan ƙarin ne yayin taya ma'aikata murnar 'Ranar ma'aikata ta duniya' ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262