Sallar Idi: Abun da yasa muka bijirewa Sarkin Musulmi – Shehin da ya jagoranci sallah a Sokoto
- Sheikh Musa Lukwa ya magantu kan bijirewa umurnin Sultan na Sokoto kan sallar idi na karamar sallah
- Ya bayyana cewa manyan malamai da dama sun tabbatar da ganin wata kuma Annabi ya yi umurnin yin azumi tare da ajiye shi da zarar an ga jinjirin wata
- Lukwa dai ya jagoranci magoya bayansa wajen yin Sallar Idi a jihar Sokoto a yau Lahadi, 1 ga watan Mayu
Sokoto - Malamin musulunci da ya jagoranci mabiyansa wajen gudanar da sallar Idi a ranar Lahadi, 1 ga watan Mayu, Sheikh Musa Lukwa, ya kare kansa kan abun da ya aikata.
Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Litinin, 2 ga watan Mayu a matsayin ranar karamar sallah.
Sultan ya sanar da cewar ba a ga jinjirin watar Shawwal na1443AH ba a ranar Asabar, amma Sheikh Lukwa ya ce matsayar Sultan din ba daidai bane.
Ya bayyana ma jaridar Daily Trust cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Wani lakcara a jami’ar Danfodio, Dr. Maigari, ma ya tabbatar da ganin jinjirin watan a jami’ar kuma akwai rahotanni kan ganin jinjirin watan daga kimanin garuruwa 10 a Jega, jihar Kebbi, wanda babban limamin Jega, Malam Bashar ya tabbatar.
“Kuma Sheikh Dahiru Bauchi ma ya tabbatar da ganin jinjirin watan a wurare da dama a kasar.
“Don haka mun yi sallar idinmu daidai da koyarwar Annabin tsira wanda ya bukace mu da mu yi azumi sannan mu sha ruwa da zaran an ga jinjirin wata. An yarda cewa dole musulmi ya bi shugabanninmu musamman ma Sultan amma bisa sharadin cewa bai saba ma Allah da Mazansa ba.
“Ba zai yiwu ka zantar da hukunci bisa hujjar kimiyya ba saboda ya sabawa addininmu kuma shi kansa Imam Malik ya yi hani ga hakan.”
Kan ko sun sanar da abun da suka lura ga kwamitin neman wata, Sheikh Lukwa ya ce babu amfanin aikata haka saboda sun rigada sun yanke shawara da zuciyarsu.
Ya tuna misalai da dama inda kwamitin ya yi watsi da irin wannan rahotannin.
“A 2011, wani lamari makamancin haka ya faru. An ga jinjirin wata a wurare da dama sannan aka sanar da kwamitin amma da suka gabatar da rahotonsu ga Sultan, sai ya yi watsi da shi. Wannan ne dalilin da yasa shugaban kwamitin, Farfesa A A Gwandu ya yi murabus a lokacin.
“Sannan akwai lokacin da aka ga jinjirin wata a yankin Mabera, aka kuma sanar da mai unguwar Mabera wanda ya gabatar da rahoto ga Hakimin Gagi inda ya kira sakataren fadar sarki sau da dam aba tare da amsa ba.
Sai ya rubuta wasika zuwa ga Sultan amma Sultan ya amsa da cewar, za a ga jinjirin wata ne a washegarin ranar. Na ga amsar. Ba za mu iya biyayya ga mutumin da yake sabawa Allah da manzonsa ba.”
Legit Hausa ta zanta da wani daga cikin mabiyan malamin mai suna Nisfu Hayat, wanda ya daga cikin wadanda suka sallaci Idi a yau, inda ya bayyana lallai abun da suka yi shine daidai.
Ga yadda hirar ta kaya:
Shin baku ganin wannan abun da suka yi kaskantar da sarkin musulmi dama majalisar koli ta musulunci ta kasa bane, sai ya ce:
"Mu a fahimtarmu, Bin Allah da manzon sa ne agaban bin kowane mutum a doron kasa, kowaye kuma ko miye matsayinsa, Lokacin da yace an ga wata da muka ganshi a tare dashi muka dauka, yanzun kuma da aka ganshi yace bai yarda ba, bazamu bishi akan hakan ba. Qasqanci ai duk yana bayan qin bin umarnin Allah da Manzonsa. Mu in dae ba Allah da Manzonsa muka sabawa ba. Alhamdulillah."
To amma baku ganin biyayya ga shugabannin Musulmai wani umurni ne na Manzon Allah?
"Ai zancen haka yake, Duk zancensa Allah da manzonsa ne ba wai ra,ayinsa ne yake bi ba.
"Haka zalika Sabamasa akan kuskure shima umarni ne na manzon Allah. S.a.w."
Amma mutane sun halarci masallacin Idin da yawa kuma me suke cewa game da yin Sallah yau?
"Amsarka itace Eh, Dubban mutane kuwa. Alhamdulillah muke cewa."
Daga karshe za mu so ka fada mana adireshi ko sunan anguwar da aka gudanar da sallah
"Mabera arewa, Shiyar Mana."
Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmi, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto
A baya mun ji cewa wasu Musulmai a jihar Sokoto sun gudanar da Sallar Idi yau Lahadi wanda ya saɓa wa umarnin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Eid-ul-Fitr.
Daily trust ta rahoto cewa a ranar Asabar, Sarkin Musulmai ya sanar da cewa ba'a ga jinjirin watan Shawwa 1443AH ba a sassan Najeriya.
Asali: Legit.ng