An ji labarin mutuwar Fasto, makonni 8 bayan ‘Yan garkuwa da mutane sun dauke shi

An ji labarin mutuwar Fasto, makonni 8 bayan ‘Yan garkuwa da mutane sun dauke shi

  • Rabaren Joseph Akete da aka yi garkuwa da shi kwanakin baya a Kaduna, ya ce ga garinku nan
  • Faston ya mutu ne dai a yayin da ‘yan bindiga suke cigaba da tsare shi domin samun kudin fansa
  • Limaman cocin Katolika na jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar Faston tun a cikin watan Afrilu

Kaduna - Joseph Akete na babban cocin darikar Katolika na St. John da ke garin Kudenda a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna, ya bar Duniya.

Punch ta fitar da wani rahoto a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu 2022 da ya bayyana cewa Rabaren Joseph Akete ya mutu ne a wajen wadanda suka sace shi.

Babban limamin Katolika na jihar Kaduna, Rev. Fr. Christian Okewu Emmanuel, shi ya sanar da manema labarai cewa Faston ya rasu da ya zanta da su jiya.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Kamar yadda Christian Okewu Emmanuel ya shaidawa ‘yan jarida a ranar Laraba, Rabaren Akete ya mutu tun kusan tsawon makonni uku da suka gabata.

Tsakanin ranar 18 da ranar 20 ga watan Afrilun da ya wuce ake tunanin Rabaren Akete ya mutu.

Dama can Faston bai da lafiya

A cewar Rabaren Christian Okewu Emmanuel, tun kafin ‘yan bindiga su yi garkuwa da Faston na Kudenda, yana fama rashin lafiya, har yana shan magani.

Faston Kaduna
Wani cocin Katolika a Najeriya Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Amma da aka zo daukarsa, ‘yan bindigan ba su bar malamin addinin ya tafi da magungunansa ba.

Babban Limamin na mabiya Katolika ya ce a gaban Marigayin aka hallaka ‘danuwansa na jini, ganin hakan ya sa rashin lafiyansa ya kara tabarbarewa.

A karshe Joseph Akete ya ce ga garinku nan, ya mutu alhali yana tsare a hannun ‘yan bindiga. Har zuwa yanzu iyali da 'yanuwansa ba su ga gawan sa ba.

Kara karanta wannan

An yi ram da mai mulki a Kaduna yana dauke da AK-47 kusa da sansanin ‘Yan bindiga

Ta'aziyyar Limamin Katolika

“Ba mu karbo gawarsa ba, amma mun tabbatar da mutuwarsa. Wadanda aka yi garkuwa da su tare, sun shaida mana cewa sun gan shi ya mutu.”

- Christian Okewu Emmanuel

A madadin daukacin mabiya darikar Katolika na Kaduna, Rabaren Matthew Man-Oso Ndagoso ya aika da sakon ta’aziyya ga iyalin marigayin da almajiransa.

Jaridar Sahara Reporters ta ce nan gaba za a sanar da lokacin da za ayi a wa Faston jana’iza.

Babu zaman lafiya a Najeriya

A dazu mu ka kawo rahoto da ya nuna cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Olu Falae ya na da ra’ayin cewa halin da ake ciki a Najeriya ya tabarbare.

Cif Falae yake cewa yanzu rayuwa ta zama babu tabbas, ana iya kashe mutum a farat daya. Falae ya ce a yau, idan ka fi makwabacinka karfi, sai ka hallaka shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel