Da Dumi-Dumi: Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmi, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto

Da Dumi-Dumi: Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmi, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto

  • Wasu al'umma mabiya Addinin Musulunci a Sokoto sun gudanar da Sallar Eid-El-Fitr yau Lahadi inda suka saba wa umarnin Sarkin Musulmai
  • Mutanen waɗan da mafi yawancin su mabiya Shekih Musa Lukwa ne, sun yi Sallah da misalim ƙarfe 8:00 na safe bayan tabbatar da ganin wata
  • Sheikh Lukwa ya bayyana cewa mutane da dama sun ga jinjirin watan Shawwal a sassan Sokoto da wasu kasashen waje

Sokoto - Wasu Musulmai a jihar Sokoto sun gudanar da Sallar Idi yau Lahadi wanda ya saɓa wa umarnin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Eid-ul-Fitr.

Daily trust ta rahoto cewa a ranar Asabar, Sarkin Musulmai ya sanar da cewa ba'a ga jinjirin watan Shawwa 1443AH ba a sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ministan kimiyya da fasaha ya yi murabus daga gwamnatin Buhari

Sallar Idi a Sokoto.
Da Dumi-Dumi: Wasu Musulmai a Sokoto sun yi watsi da umarnin Sultan, sun gudanar da Sallah yau Lahadi Hoto: Dokin karfe tv/facebook
Asali: Facebook

Mafi yawan Musulman, waɗan da mabiya ne ga Sheikh Musa Lukwa, sun gudanar da Sallar idi wato ƙaramar Sallah da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi.

Da yake zantawa da wakilim jaridar, Sheikh Lukwa, ya ce sun samu sahihan bayanan ganin jinjirin watan Shawwal a wasu sassan Najeriya da wasu ƙasashen waje.

A jawabinsa, yace Musulmai sun ga wata jihohi biyar na Jamhuriyar Nijar, inda ya ƙara da cewa:

"Na kalli bidiyon shugaban ƙasar su (Nijar) lokacin da yake ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar idin ƙaramr Sallah, kuma an ga wata a ƙasar Afghanistan, Mali da wasu ƙasahen Afirka kuma sun gudanar da Sallah yau."
"A nan Sokoto, Mutum Takwas sun tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a ƙauyen Fakku da ke ƙaramar hukumar Kebbe, cikinsu har da babban limamin su."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Malaman makarantun Poly sun bi sahu, ASUP ta sanar da shiga yajin aiki

"Haka nan mutum 50 sun tabbatar da ganin jinjirin wata a ƙauyen Wauru. ƙaramar hukumar Gada duk a nan jihar Sokoto."

Legit.ng Hausa ta samu zantawa da ɗaya daga cikin mabiyan da suka gudanar da Sallah wanda ya bayyana sunnasa da Nisfu Hayat, ya shaida mana cewa matsalar ganin wata a Najeriya ba yau aka fara ba.

Hayat wanda ya ayyana yau a matsayin ranar Sallah a wajensa ya shaida wa wakilin mu cewa:

"Gaskiya matsalar ganin wata a Najeriya tana da girma zan iya cewa Sarkin Musulmi ne ya assasa ta, ba shi ne basarake na farko ba, wasu sun gabace shi amma shi aka fara samun matsala da shi."
"Abun da son rai a ciki, anan Sokoto kowa ya san akwai wani Malami da ya fito ya ce ya bar kwamitim duban wata domin akwai matsala a ciki."
Mutanen da suka yi Sallah a Sokoto.
Da Dumi-Dumi: Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmi, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto Hoto: Yola TV/facebook
Asali: Facebook

Shin meyasa Sheikh Lukwa ya ɗauki wannan matakin?

Ya ƙara da cewa Sheikh Lukwa Malaminsa ne da yake bin Sunnah, kuma tun ba yanzu ba yake kai korafi kan ganin wata ga Kwamiti amma ba'a duba wa.

Kara karanta wannan

Zaura ya bi zabin Ganduje ya janye daga takarar gwamnan Kano, zai kwace kujerar Shekarau a 2023

Ya shaida mana cewa:

"Malam Musa Lukwa malami ne mai bin aƙidar magabata (Salaf), yana kai korafe-korafe idan an ga wata yana sanar da Sarki amma ba'a dubawa, dalilin shi ne sun maida ganin watan a kimiyyance."
"Mun yi Sallah yau saboda an ga wata a Nijar, an ganshi a wasu sassan Najeriya har da nan Sokoto."

A wani labarin kuma mun kawo yadda aka gudanar da Sallar Idi ƙarama a jamhuriyar Nijar biyo bayan ganin wata da mhukunta suka sanar a ƙasar

A yau Lahadi, 1 ga watan Maris ne al’ummar Musulmi suka yi sallar idi a Jamhuriyar Nijar bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a kasar, lamarin da ya kawo karshen azumin Ramadana.

Ba a yi sallah ba a kasashe da dama ciki harda Saudiyya da Najeriya sakamakon rashin ganin wata. Hakan na nufin sai gobe Litinin za a sallaci idi a kasashen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262