Yau take ranar sallah: Hotunan yadda al'ummar Musulmi suka sallaci Idi a Nijar

Yau take ranar sallah: Hotunan yadda al'ummar Musulmi suka sallaci Idi a Nijar

  • Al'ummar Musulmi a Jumhuriyar Nijar sun yi bikin karamar Sallah a yau Lahadi, 1 ga watan Mayu
  • Hakan ya biyo bayan sanar da batun ganin jinjirin watan Shawwal da majalisar koli ta musulunci da gwamnatin jihar ta yi a ranar Asabar
  • A hotunan da suka yadu a shafukan sadarwa, an gano mutane a masallacin idi cikin shiga ta alfarma

Nijar - A yau Lahadi, 1 ga watan Mayu ne al’ummar Musulmi suka yi sallar idi a Jamhuriyar Nijar bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a kasar, lamarin da ya kawo karshen azumin Ramadana a kasar, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

Al’ummar kasar daga bangarori daban-daban sun tabbatar da ganin jinjirin watan na Shawwal a daren ranar Asabar, 30 ga watan Afrilu, inda majalisar koli ta musulunci da gwamnatin kasar suka tabbatar da hakan bayan gudanar da cikakken bincike.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisar zartarwa ta ASUU na tattaunawa, ta yuwu a kara wa'adin yajin aiki

Yau take ranar sallah: Hotunan yadda al'ummar Musulmi suka sallaci Idi a Nijar
Yau take ranar sallah Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Ba a yi sallah ba a kasashe da dama ciki harda Saudiyya da Najeriya sakamakon rashin ganin wata. Hakan na nufin sai gobe Litinin za a sallaci idi a kasashen.

A hotunan da BBC Hausa ta wallafa, an gano al’ummar musulmi manya da yara a masallacin idi cikin shiga ta alfarma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga hotunan a kasa:

Yau take ranar sallah: Hotunan yadda al'ummar Musulmi suka sallaci Idi a Nijar
Al'ummar Musulmi sun sallaci Idi a Nijar Hoto: BBC Hausa

Wasu Musulmai a Sokoto sun yi watsi da umarnin Sultan, sun gudanar da Sallah yau Lahadi

A wani labarin, mun ji cewa wasu Musulmai a jihar Sokoto sun gudanar da Sallar Idi yau Lahadi wanda ya saɓa wa umarnin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Eid-ul-Fitr.

Daily trust ta rahoto cewa a ranar Asabar, Sarkin Musulmai ya sanar da cewa ba'a ga jinjirin watan Shawwa 1443AH ba a sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

Gaskiyan abinda ya faru tsakanin Malam Musa Lukuwa da yan kwamitin ganin wata, Simwal Jibrin

Mafi yawan Musulman, waɗan da mabiya ne ga Sheikh Musa Lukwa, sun gudanar da Sallar idi wato ƙaramar Sallah da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel