Sallah: Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Duba Jinjirin Wata

Sallah: Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Duba Jinjirin Wata

  • Kwamitin Kolin Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, karkashin Shugbancin Sarkin Musulmi ta umurci yan Najeriya su fara neman jinjirin watan Shawwal yau Asabar bayan faduwar rana
  • NSCIA ta taya musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan ta kuma yi kira ga yan kasuwa su saukaka farashin kayan abinci
  • Kwamitin Kolin na Musuluncin ta kuma shawarci Gwamnatin Tarayya da kungiyar ASUU su yi sulhu domin a bude makarantu

Kwamitin Kolin Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ta taya musulmi murnar Sallah Karama da kammala azumin watan Ramadan, rahoton Premium Times.

A cikin sanarwar da Direktan Gudanar Da Ayyuka, Zubairu Usman-Ugwu ya fitar a ranar Juma'a, NSCIA ta umurci musulmi su aiwatar da darrusan da suka koya a ramadan, wanda shine tallafawa marasa karfi.

Sallah: Ranar Asabar Za a Fara Neman Wata, In Ji Sarkin Musulmi
Sallah: Ranar Asabar Za a Fara Neman Wata, Sarkin Musulmi. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

Ana bikin sallah karama ne a kowanne shekara bayan kammala azumin watan Ramadan a duk fadin duniya.

Kara karanta wannan

Kotu ta jefa Ma'aikatan banki 2 kan laifin sace miliyoyin kudi na kwastoman da ya mutu

Sanarwar ta umurci musulmi su fara neman jinjirin watan Shawwal 1443 AH nan take bayan rana ta fadi a ranar 30 ga watan Afrilu, wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Ramadan.

NSCIA ta yi kira ga musulmi kada su kara farashin kayan abinci kuma su shiga zabe a yi da su

NSCIA ta yi kira ga al'ummar musulmi kada su kara farashin kayayyakin abinci da tuni ma sunyi tsada a sassan kasar.

Mr Usman-Ugwu ya yi kira ga musulmi su nemi takarar kujerun siyassa kuma su shiga a dama da su wurin zaben shugabanni ta hanyar mallakar katin zabe wato PVC.

Kungiyar ta kuma yi kira ga Kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU da gwamnatin tarayyar Najeriya su kawo karshen yakin aikin da ya dakatar da karatu a kasar.

Kara karanta wannan

Sallah: Tinubu ya gwangwaje Musulmai da buhunan shinkafa 3,000 a Nasarawa

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

A wani rahoton kun ji cewa Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN sun ja kunnen jam’iyyun siyasa akan tsayar da ‘yan takarar su duk masu addinai daya a zaben 2023 da ke karatowa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito kungiyar ta ce kada duk ‘yan takarar su kasance musulmai ko kuma duk kiristoci don hakan na iya yamutsa siyasa a kasar.

Shugaban CAN, Dr Samson Ayokunle ya yi wannan jawabin ne yayin da ya jagoranci wata ziyara da su ka kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel