Bidiyo: An Shiga Ruɗani Bayan An Hangi Wata Budurwa Zaune Shiru a Tsakiyar Rafi a Jami'a Tsawon Awa 6

Bidiyo: An Shiga Ruɗani Bayan An Hangi Wata Budurwa Zaune Shiru a Tsakiyar Rafi a Jami'a Tsawon Awa 6

  • Wata budurwa ta janyo rudani a jami'ar KNUST bayan an hange ta zaune a tsakiyar rafi a ma suna Bibini
  • An ta yada hotunan yarinyar tsakanin dalibai inda suke ta mamakin abin da ke faruwa da ita
  • Daga bisani an gano cewa yarinyar daliba ce mai karatun digiri na biyu a makarantar kuma abin da ta yi cikin aiki ne na kayatar da mutane

Dalibai da dama a Jami'ar KImiyya da Fasaha ta Jami'ar Nkrumah, Ghana, (KNUST) sun shiga rudani a yayin da aka hangi wata budurwa sanya da kaya tana zaune shiru a tsakiyar Rafin Bibini a jami'ar.

A cewar Voice of KNUST da ya rahoto lamarin a shafinsa na Twitter, yarinyar ta zauna cikin ruwan tsawon awa shida, abin ya kuma bazu a duk jami'an.

Bidiyo: An Shiga Ruɗani Bayan An Hangi Wata Budurwa Zaune Shiru a Tsakiyar Rafi a Jami'a Tsawon Awa 6
An Shiga Ruɗani Bayan An Hangi Wata Budurwa Zaune Shiru a Tsakiyar Rafi a Jami'a Tsawon Awa 6, Bidiyon Ya Bazu. Hoto: VOICE_of_KNUST/Twitter
Asali: UGC

Daga baya an bayyana cewa abin da ta aikata mai daure kai ba komai bane illa wani sashi na binciken ilimi da wasu daliban masu digiri na biyu ke yi a jami'ar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi dala 75,000 a hedkwatar APC

"Yarinyar da ta zaune a cikin Rafin Bibini tsawon awa 6 ba tayi ne don tsorata mutane ba amma wani sashi ne na binciken ilimi da wasu daliba masu digiri ta biyu ke yi," a cewar Voice of KNUST.

Wasu mutane a dandalin sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu

@WiafeAk3nt3ng yayin mayar da martani ga @VOICE_of_KNUST ta ce:

"Ilimin Art fadi gare shi ... ga wadanda ke sukar tsangar fine arts na knust ba su san cewa art yana da fadi sosai ba kuma akwai sabon salo da ke tasowa da nan gaba zai bazu lokacin za su gane kaifin tunanin jami'ar."

@Conti_Bharon ya ce:

"Ta yaya zama a cikin rafi zai zama wani binciken ilimi mai amfani. Shin kafar ta na gwada zurfin rafin ne ko suna bukatar dan adama ya gwada sanyi ko zafin ruwan ne a lokuta daban-daban. Akwai na'ura daban-daban da za su iya. Ya zaka fada min wannan labarin?"

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164