Matsalar Tsaro: Kasar Syria yanzu ta fi Najeriya tsaro da zaman lafiya

Matsalar Tsaro: Kasar Syria yanzu ta fi Najeriya tsaro da zaman lafiya

  • Dan takaran kujerar shugaban kasa yace a yanzu dai kasar Syriya ta fi Najeriya zaman lafiya
  • Peter Obi yace gwamnatin Buhari karban bashin kudi da rabawa gwamnonin kawai ta iya
  • A cewarsa, muddin ba'a sauya wannan gwamnati ba wannan matsalar tsaro ba zai kare ba

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ma niyyar takara kujeran shugaban kasa karkahin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Peter Obi, a ranar Alhamis yace kasar Syria yanzu tafi Najeriya zaman lafiya.

Obi ya bayyana hakan ne yayinda ya ziyarc dleget din PDP na jihar Imo kan niyyar takararsa, rahoton Vanguard.

Peter Obi ya gana da su ne a hedkwatar jam'iyyar dake titin Okigwe, Owerri.

Matsalar Tsaro: Kasar Syria yanzu ta fi Najeriya tsaro da zaman lafiya
Matsalar Tsaro: Kasar Syria yanzu ta fi Najeriya tsaro da zaman lafiya
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Rundunar Sojin Najeriya Za Ta Tura Sojoji 197 Zuwa Gambia Don Samar Da Zaman Lafiya

Tsohon gwamnan yace rashin tsaron dake Najeriya yanzu ya wuce tsammani karkashin mulkin jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Ya kara da cewa matsalolin Najeriya sun yi tsanani saboda gwamnati APc raba kudi kawai take yi maimakon inganta tattalin arziki.

A cewarsa:

"Za ka waye gari kullum a Najeriya kaji an kashe mutane, irin abinda dake faruwa a Afghanistan da Pakistan. Kai yanzu Syria ta fi Najeriya, kuma abin kara baci zai yi."
"Najeriya ta ci basussukan dake ba zamu taba iya biya cikin shekaru uku masu zuwa ba. Mafita daya itace mu samar da tattalin arziki mai kirkira da samar da abubuwa, ba na raba kudi ba."
"Abinda gwamnatin APc ta iya kadai shine raba kudi ba kirkirar komai ba. Hanyar farko na samar da tsaro shine samar da aikin yi."

Tsanantar harin 'yan bindiga: Mazauna kauyukan Zamfara suna kaura daga gidajensu

Mazauna kauyen Magazu da kewaye a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun fara barin gidajensu na gado sakamakon tsanantar farmakin 'yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Ya Bayyana Dalilan Saka N100m a Matsayin Kudin Fom Din Takarar Shugaban Kasa

Wasu daga cikin mazauna yankunan an gansu tsaitaye a bakin titi da 'ya'yansu, kayansu a daddurae da dabbobinsu biye da su.

Premium Times ta ruwaito cewa, sun sha alwashin ba za su sake komawa gidajensu ba har sai tsaro ya tabbata a yankin.

Yankin Magazu ya kasance madaddalar 'yan bindiga inda suka matsantawa domin kua tun ranar Litinin da ta gabata suka kai farmaki har zuwa yau babu sauki, lamarin da ke cigaba da kawo rashin rayuka da salwantar dukiyoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel