Rundunar Sojin Najeriya Za Ta Tura Sojoji 197 Zuwa Gambia Don Samar Da Zaman Lafiya

Rundunar Sojin Najeriya Za Ta Tura Sojoji 197 Zuwa Gambia Don Samar Da Zaman Lafiya

  • Rundunar sojin Najeriya na shirin tura dakarunta 197 zuwa kasar Gambia don samar da zaman lafiya
  • Shugaban ayyuka na hedkwatar sojin, Olufemi Akinjobi ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin taron yaye wasu sojoji
  • A cewar Akinjobi, Najeriya ta jajirce wurin ganin ta samar da nagartattun dakaru masu kawo zaman lafiya da tsaro a kasashen duniya

Kaduna - Rundunar sojin Najeriya tana shirin tura dakarunta 197 karkashin shirin kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka na Yamma, ECOWAS na kawo zaman lafiya a Gambia, Premium Times ta ruwaito.

Shugaban ayyuka na Hedkwatar soji, Olufemi Akinjobi, wanda manjo janar ne, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin taron yaye dalibai na Nigerian Company 7 wanda nan ba da jimawa ba za su jagoranci kananun kasahen Afirka na Yamma.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ƴan Siyasan Najeriya Sun Fi Boko Haram Hatsari, In Ji SSANU

Rundunar Sojin Najeriya Za Ta Tura Sojoji 197 Zuwa Gambia Don Samar Da Zaman Lafiya
Najeriya za ta tura sojoji 197 zuwa Gambia. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

An yi taron ne a Cibiyar Zaman Lafiya da Shugabancin Kasa da Kasa na Martin Luther Agwai da ke Jaji a cikin Jihar Kaduna.

Ba wannan bane karo na farko

NAN ta ruwaito yadda kafin yanzu Najeriya ta tura kamfanoni 6 daban-daban zuwa kasar Gambia.

A cewar Akinjobi, Najeriya ta jajirce wurin ganin ta samar da dakarun da ke kawo zaman lafiya a duniya da tsaro.

NAN ra ruwaito yadda cikin dakaru 197 da ake shirin turawa Gambia, 185 sojoji ne kananu yayin da 12 manyan sojoji ne.

Akinjobi wanda ya samu wakilcin Zakari Abubakar, manjo janar kuma darektan harkokin samar da zaman lafiya a hedkwatar sojoji.

Najeriya ta dade tana samun nasarori na samar da zaman lafiya

Ya bayyana yadda Najeriya ta samu nasarori bayan shiga shirye-shirye 40 na samar da zaman a fadin duniya, kuma ta tura fiye da sojojinta 100,000 tun daga 1960.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya tsige manyan sarakuna 2, da hakimi bisa taimakawa 'yan bindiga

Dama tun farko kwamandan cibiyar, Manjo Janar Auwal Fagge ya bayyana yadda cikin makwanni 4 da suka gabata suka horar da wasu dakaru akan harkokin zaman lafiya.

Ya kuma bukaci dakarun da su kasance wakilan Najeriya na kwarai a duk inda suka tsinci kawunansu sannan su yi kokarin aikata abubuwan da suka koya a cibiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel