Kada ka fito takara: Tsaffin ministoci da masoya sun gargadi Goodluck Jonathan

Kada ka fito takara: Tsaffin ministoci da masoya sun gargadi Goodluck Jonathan

  • Wasu tsaffin makusantan Goodluck Jonathan sun bashi shawarar kada yace zai fito takara
  • Kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na shirin komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Jonathan ya fito ya yi jawabi da masu bukatar ya fito takara ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja

Tsaffin ministoci da tsaffin hadiman tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, suna bashi shawaran yayi watsi da kiran da ake masa na ya fito takarar kujeran shugaban kasa a 2023.

A cewar TheNation, majiyoyi dake kusa da tsohon shugaban kasa a ranar Juma'a a Abuja sun bayyana cewa manyan masu bashi shawara da tsaffin ministoci sun bayyana masa ranar Laraba cewa kada ya sake ya koma APC.

A cewar majiyoyin, tun da har yanzu shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin APC basu bashi amince masa tikitin kai tsaye ba, kada ya yaudaru.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba

Goodluck Jonathan
Kada ka fito takara: Tsaffin ministoci da masoya sun gargadi Goodluck Jonathan
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wasu daga cikin mashawartansa, ya bayyana karara sauran yan takaran APC ba zasu yarda a mikawa Jonathan tikicin kai tsaye ba.

Daya daga cikin majiyoyin yace:

"Mun yi dubi cikin duka zabin da Jonathan ke da su kuma mun bashi shawara yayi watsi da shirin komawa APC."
"Kawo ranar Laraba, bai samu tabbaci daga wajen Buhari ko APC cewa zasu bashi tikitin ittifaki ba."
"Ka ga dai ba zai iya cin zaben fidda gwanin APC ba saboda bai da mabiya ana sauran wata daya zabukan.

Wata majiyar tace:

"Wasu tsaffin makusantansa sun fada masa gwanda ya cigaba da zama dattijo a idon duniya da ya cusa kansa cikin zaben shugaban kasan 2023."
"Musamman mun fada masa ba zama dole mu goyi bayansa ba idan ya koma APCn da suka tsinewa gwamnatinsa, suka caccakesa kuma suka garkame wasu daga cikinsu."

Kara karanta wannan

2023: Adams Oshiomhole Ya Fayyace Gaskiya Kan Batun Takararsa Na Shugaban Kasa

Har yanzu ina shawarar takara, ku dakace ni: Goodluck Jonathan

Bayan zanga-zanga da ihun sunansa da sassafe, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, a ranar Juma'a ya fito don jawabi ga yan zanga-zangan da suka dira ofishinsa.

A jawabinsa, Jonathan ya bukaci matasan Najeriya sun zurfafa ra'ayinsu cikin siyasar Najeriya, rahoton Vanguard.

Tsohon shugaban kasan yace lokaci ya yi da ya kamata matasa su ci gajiyar dokar 'Not Too Young To Run Act'.

Yace yana sane cewa sun zo kira gareshi yayi takara amma ba zai ayyana niyyarsa yanzu ba saboda yana shawara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng