Bayan Shekara biyu, Buhari ya amince yan Najeriya su je masa yawon Sallah, an gindaya sharuɗda

Bayan Shekara biyu, Buhari ya amince yan Najeriya su je masa yawon Sallah, an gindaya sharuɗda

  • Bayan tsawon shekara biyu Fadar shugaban ƙasa ta ce bana za'a gudanar da al'adar barka da Sallah tare da shugaba Buhari
  • Kakakin shugaban ƙasan, Malam Garba Shehu, ya ce duk da an cimma yaƙi da korona, duk wanda aka gayyata sai ya cika sharuɗɗa
  • Shehu ya ce kowane baƙon da aka gayyata sai ya yi gwajin Korona kuma tilas da sanya takunkumi

Abuja - Shekara biyu bayan Annobar COVID19 ta tsaida komai cak a duniya, al'adar da aka saba ta zuwan mazauna babban birnin tarayya Abuja yawon Sallah Aso Villa zai dawo a wannan Eid-El-Fitr.

A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Twitter, yace wannan matakin ya biyo bayan raguwar harbuwa da cutar mafi ƙaranci da ake samu.

Fadar shugaban ƙasa.
Bayan Shekara biyu, Buhari ya amince yan Najeriya su je masa yawon Sallah, an gindaya sharuɗda Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Tun bayan ɓarkewa Annobar Korona, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya hana kai masa ziyarar barka da Sallah a wani yunƙuri na daƙile yaduwarta.

Kara karanta wannan

2023: Wani Fitaccen ɗan kasuwa ya fito takara a NNPP, ya shirya fafatawa da Kwankwaso

Fadar shugaban ƙasa ta gindaya sharuɗɗa

Shehu ya bayyana cewa duk wanda ya samu katin gayyata, akwai bukatar ya sanya takunkumi kuma ya yi gwajin cutar COVID19 a Asibitin Aso Rock don tabbatar ba ya ɗauke da ita kafin ya shiga.

Ya ce shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai shirya tarban kusan mutum 100 a ranar Sallah (Lahadi ko Litinin) ya danganta da sanarwan kwamitin duban wata.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Baƙin da aka gayyata zuwa wurin bisa jagorancin Ministan Abuja, Muhammad Bello, sun haɗa da Sakataren gwamnati, shugaban ma'aikata, Sanata da mambobin majaisa na Abuja."
"Sai kuma shugabannin ɓangaren Sharia na Abuja, Hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin tsaro, shugabannin musulmai da kirista na Abuja, sarakuna da sauran waɗan da katin gayyata ya isa gare su."

Kara karanta wannan

2023: Sabon ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayyana aniyarsa a APC, ya nemi a rage masa kuɗin Fom

A wani labarin kuma Jerin Sunayen gwamnonin APC, PDP da suka shirya janye wa Jonathan takarar shugaban ƙasa a 2023

Wasu fitattun yan siyasa sun shirya canza kudirinsu na neman takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Wasu gwamnoni biyu masu ci sun yanke cewa zasu iya janye wa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262