Innalillahi: Allah ya yiwa hamshakin attajiri a Kano, Tahir Fadlullah rasuwa
- Labarin da ke iso mu ya bayyana cewa, wani hamshakin attajirin jihar Kano ya kwanta dama a kasar Lebanon
- Tahir Fadlullah, wani hamshakin attajiri mamallkin otal din Tahir Guest Palace ya rasu ne a kasar haihuwarsa
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, za a binne Faldullah a jihar Kano, inda ya rayu tsawon shekaru da dama
Lebanon - Hamshakin attajirin nan mai shahararren otal din Tahir Guest Palace da ke Kano, Tahir Fadlullah, ya rasu.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da rasuwar Fadlullah ta shafinsa na Instagram da safiyar yau Juma’a.
Ya bayyana rasuwar mamallakin otal din a matsayin abin razanarwa, kuma ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya kuma ba iyalansa hakurin rashi.
An samu labarin cewa Mista Fadlullah, wanda ya rasu a kasarsa ta haihuwa, Lebanon, za a binne shi ne a birnin Kano ta Najeriya, inda ya rayu tsawon shekaru da dama.
Allah ya yi wa wani Sarkin Gargajiya a Osun rasuwa
Basaraken gargajiya na ƙasar Ikoyi a jihar Osun, Oba Yisau Bamitale Oyetunji Otunla, ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Basaraken wanda aka naɗa wa rawanin Sarauta a shekarar 1987, ya shafe shekaru 35 a kan karagar Sarauta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mazauna ƙasar Ikoyi sun ba da kyakkyawar shaida a kan marigayi Sarkin, sun ce mulkinsa ya kasance na zaman lafiya.
Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na BUK Rasuwa
A wani labarun na daban, kun ji cewa, tsohon shugaban rikon kwarya na Jami'ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Danjuma Maiwada, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.
Maiwada, wanda ya yi aiki na kankanin lokaci a matsayin shugaban riko na BUK a 2004, dan asalin Jihar Katsina ne amma mafi rayuwarsa a Kano ne inda ya ke koyarwa a jami'ar tun 1976 a tsangayar ilimi.
A shekarar 2015, ya yi aiki a matsayin shugaban riko na jami'an Northwest University, Kano da yanzu ake kira Jami'ar Yusuf Maitama Sule.
Asali: Legit.ng