An damke sojan da ke hada kai da ISWAP, ya bindige kansa ana shirin mika shi bariki

An damke sojan da ke hada kai da ISWAP, ya bindige kansa ana shirin mika shi bariki

  • Jami'an binciken sirri na sojin Najeriya sun kama wani soja da ke hada kai da mayakan ta'addanci na ISWAP wurin kai hare-hare
  • Kamar yadda bincike ya nuna, yana da hannu wurin saka bama-bamai a gidajen karuwai da na giya da aka yi a Geidam da Gashua dake Yobe
  • Sai dai bayan saka masa ankwa da shirin mika shi bariki, cike da kwarewa sojan ya kwace bindiga tare da harbe kansa

Yobe - Hukumomi sun damke wani soja da ke hada kai da mayakan ta'addanci na ISWAP wurin kai farmaki amma ya bindige kansa yayin da ake kokarin mika shi bariki.

PRNigeria ta tattaro cewa, sojan yana daya daga cikin sojojin bataliyoyin rundunar sojan Najeriya da ke yaki da rashin tsaro a arewa maso gabas kuma jami'an binciken sirri na sojoji ne suka gano hannunsa a farmakin kwanakin nan da aka kai gidajen karuwai da na giya da ke Geidam da Gashua a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abj-Kad: Daya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hannun 'yan bindiga

An damke sojan da ke hada kai da ISWAP, ya bindige kansa ana shirin mika shi bariki
An damke sojan da ke hada kai da ISWAP, ya bindige kansa ana shirin mika shi bariki. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
"Yana da hannu cikin farmakin kwanakin nan na Geidam da Gashua a jihar Yobe. An kama shi yayin da yake yunkurin tserewa bayan ya gane cewa jami'an binciken sirri suna bibiyar lamurransa da 'yan ta'addan.
“Bayan an saka masa ankwa, cike da kwarewa ya kwace bindiga daga hannun daya daga cikin wadanda ke tsare da shi kuma ya kashe kansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A halin yanzu, ana bincike domin kama sauran wadanda ake zargi a cikin rundunar sojin," majiyar ta sanar da PRNigeria.

Borno: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari ana tsaka da shagalin biki

A wani labari na daban, an rasa ran mutum daya inda wasu da dama suka jigata yayin da mayakan ta'addancin Boko Haram/ISWAP suka kai farmaki wurin wani shagalin aure a kauyen Kindila na karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Kamar yadda wata majiya ta sanar, maharan sun bayyana a cikin manyan motoci biyu kuma suka tare hanyar fita yayin da suke ta harbe-harbe kan duk wanda suka samu, al'amarin da yasa mutane suka dinga gudu domin tseratar da rayukansu, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

"Daga bisani miyagun sun halaka wani dan banga mai suna Suleiman sa'in da suka tafi da shi. An ga gawar marigayin," wata majiya ta tabbatar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel