Sama da rayuka 100 sun salwanta sakamakon gobara da ta tashi a matatar man fetur din sata a Imo

Sama da rayuka 100 sun salwanta sakamakon gobara da ta tashi a matatar man fetur din sata a Imo

  • Sama da rayukan mutum 100 ne suka salwanta sakamakon mummunar gobarar da ta tashi a matatar man fetur din sata a Imo
  • Lamarin ya fara wurin karfe 11 na daren Juma'a kuma matasa masu tarin yawa dake aiki a wurin sun bakunci barzahu
  • Gwamnann jihar, Hope Uzodinma ya bayyana cewa ana neman mai wurin ido ruwa jallo bayan ya cika bujensa da iska ana tsaka da ibtila'in

Imo - A kalla rayuka 100 ne suka salwanta sakamakon fashewar wani abu a matatar man fetur na sata dake Ohaji a karamar hukumar Egbema ta jihar Imo.

Lamarin, wanda ya fara wurin karfe 11 na daren Juma'a, ya yi sanadiyyar tashin gagarumar gobara a Ohaji da ke yankin Egbema, Thecable ta ruwaito.

Sama da rayuka 100 sun salwanta sakamakon gobara da ta tashi a matatar man fetur din sata a Imo
Sama da rayuka 100 sun salwanta sakamakon gobara da ta tashi a matatar man fetur din sata a Imo. Hoto daga thcable.ng
Asali: UGC

A yayin jawabi kan lamarin, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, wanda ya samu wakilcin Goodluck Opiah, kwamishinan lamurran man fetur, ya ce matasa da yawa sun rasa rayukansu sakamakon gobarar, amma har yanzu ba a kididdige yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam ya ƙara fashewa a babban birnin jihar Arewa, ya shafi mutane da dama

Kamar yadda The Guardian ta rahoto, Opiah ya ce, Okenze Onyewoke, wanda aka gano a matsayin mamallakin matatar man fetur din satan ana nemansa ido ruwa jallo.

"Mummunar gobarar ta tashi ne sakamakon diban man sata tare da tace shi a wurin, wanda hakan ya shafi sama da mutane 100 wadanda suka babbake," yace.
"A halin yanzu, ba zan iya tabbatar da yawan mamatan ba saboda iyalai da yawa sun zo sun kwashe gawawwakin 'yan uwansu.
"Baya ga wannan ibtila'in, mummunan lamarin ya halaka dabbobin da ke cikin ruwa a yankin. A baya mutanenmu duk manoma ne d masunta.
"Ku duba yanzu, hayaki ne ke fitowa daga matatun man satan. Idan wannan bai sa mutane sun daina ba, ina tunanin yankin yana tunkarar abinda ba zai iya kwatantawa ba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Ofishin Babban Bankin Najeriya, CBN, Ta Kama Da Wuta

"Da yawa daga cikin mutanen da ke wannan mugun aikin ba 'yan asalin jihobin Ribas, Bayelsa ko masu makwabtaka da mu bane. Wannan zagon-kasa ne ga mutanen mu."

Gwamna ya jajantawa iyalan mamata

A cewar jaridar Premium Times, ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da nan kunnen mazauna yankin da su kiyaye daga shiga irin wannan muguwar harka.

"Ina kira ga matasanmu da su guje wa saka kansu cikin irin wannan miyagun ayyukan. Wannan kasuwanci ne na kashe kai da suke saka kansu ciki," yace.
"A madadin gwamnatin jihar Imo, muna mika sakon ta'aziyyarmu ga iyalan wadanda suka rasa ransu. Gwamnatin Imo na addu'a Allah ya bai wa iyalan mamatan hakurin jure rashinsu."

A bangare daya, wannan lamarin na aukuwa ne yayin da masu ruwa da tsaki ke ta nuna damuwarsu kan satar man fetur da ake yi a kasar nan.

Tanka Makare da Man Fetur Ta Yi Bindiga a Tsakiyar Shagunan Mutane

Kara karanta wannan

2023: Mataimakin gwamnan Katsina ya yi murabus daga mukaminsa, zai yi takarar gwamna

A wani labari na daban, wata Tanka maƙare da man fetur ta fashe da safiyar Jumu'a a mahaɗar hanyoyi ta Upper Iweka Onitsha, jihar Anambra.

Punch ta rahoto cewa ana tsammanin duk shagunan da ginin dake wurin sun kone sakamakon wutar da ta kama bayan fashewar Tankar a hanya mai tattara mutane Onitsha-Owerri.

Wutar ta fara ci ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe kuma ta haddasa cinkoson ababen hawa a ciki da wajen birnin Onitsha.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel