Twitter ta dauki zafi yayin da wani ke neman mai kudin duniya Elon Musk ya sayi Najeriya

Twitter ta dauki zafi yayin da wani ke neman mai kudin duniya Elon Musk ya sayi Najeriya

  • Kafar Twitter ta dauki dumi yayin da 'yan Najeriya da wasu kasashe ke ci gaba da magana kan sayen Twitter
  • Wani dan Najeriya ne ya shawarci mai kudin duniya, Elon Musk ya kukuta ya sayi Najeriya kowa ya huta
  • Hakan bai yi wa masu kishin kasa dadi ba, don haka suka bayyana fushinsu game da wannan batu mara dadin ji

Najeriya - Sararin samaniyar Twitter ta kama da wuta a daren jiya Laraba lokacin da wani mai amfani da shafin ya nemi attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk ya lale kudi ya saye Najeriya.

Musk, mai kamfanin Tesla kwanaki biyu da suka gabata ya kulla wata yarjejeniya ta sayen Twitter kan kudi kusan dala biliyan 44 daga wanda ya kirkiri kafar sada zumuntan, Jack Dorsey.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Da Ke Son Gadon Kujerar Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka Adabi Najeriya

Elon Musk ya sayi Najeriya, inji 'yan twitter
Twitter ta dauki zafi yayin da wani ke neman mai kudin duniya Elon Musk ya sayi Najeriya | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Kwana daya bayan sayne twitter, Musk ya yi wani furuci mai ban mamaki, inda yace:

"Nan gaba zan saye Coca-Cola..."

Rubutun nasa dai ya jawo martani sama da 128,000, maganganun Twitter sama 43,000 da kuma dangwale sama da 673,000 a kasa.

Amma daya daga maganganu masu daukar hankali daga wani dan Najeriya, @AfamDeluxo wanda ya nemi Musk ya sayi Najeriya ya jawo cece-kuce.

Ya rubuta a kasan rubutun Musk cewa:

“Don Allah ka sayi Najeriya a ba mu wutar lantarki na sa’o’i 24. Abin da muke so kenan."

Martanin ya cinna wa Twitter wuta ba tare da fetur ba, tare da ganin maganganu iri-iri.

Martanin 'yan Twitter

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga ciki, inda wasu suka soki maganar yayin da wasu ke mamakin matsalolin Najeriya. Ga dai su kamar haka:

Kara karanta wannan

Tashin Bama-Bamai: Ya Zama Dole Ƴan Najeriya Su Fara Kare Kansu, In Ji Ƙwararru a Ɓangaren Tsaro

@callonswizzy ya ce:

"Idan ya sayi Najeriya.. Za ka zama bawa. Kuma daga nan za mu sake fara gwagwarmayar neman 'yanci."

@paulsaliu4 ya ce:

"Haka dai kanka ya daina ja. Saboda wutar lantarki ka shirya zama bawa har abada. Kana iya ba da kanka idan kana so duk da ma ba ka da amfani a Naija. To amma kasan wani abu, Musk ba zai iya siyan wannan babbar kasa ba komai arzikinsa, Naija har yanzu na da mutane masu kima irin mu."

@murimi84 ya ce:

"Abin da na kasa fahimta shi ne yadda Najeriya ke hako danyen mai kuma tana daya daga cikin masu mafi kyawun danyen mai a duniya, amma duk da haka kuna da matsalar wutar lantarki. A nan Kenya ko da kauyen karau akwai wutar lantarki 24/7, kuma yawancin wutar lantarkinmu shine makamashi ne mai kyau. Muna bukatar mu yiwa Najeriya mulkin mallaka."

@INkwerre ya ce:

"Wani lokaci, ka yi tunani da kwakwalwarka kafin magana. Nawa ne yake da shi da zai iya sayen kasa.?"

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Attajirin Duniya, Elon Musk Ya Siya Twitter Kan Kuɗi Dalla Biliyan 44

A wani labarin, kamfanin Twitter, a ranar Litinin ta tabbatar da cewa za ta sayarwa attajirin duniya Elon Musk kan kudi Dallar Amurka Biliyan 44, The Punch ta rahoto.

Sayar da kamfanin abin mamaki ne duba da cewa da farko mambobin kwamitin kamfanin sun ki amincewa Musk ya siya kamfanin dandalin sadarwar.

Hakan na zuwa ne kimanin mako guda bayan Musk ya sanar da niyarsa na siyan dandalin sada zumuntar da ya fi kauna kan $54.20 kowanne hannun jari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel