Gwamnan APC Da Ke Son Gadon Kujerar Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka Addabi Najeriya
- Gwamnan Jihar Cross Rivers Ben Ayade ya ce dimbin ma'adinan kasa da Najeriya ke da shi yasa yan ta'adda ke adabar kasar
- Ayade, yayin wata hira da aka yi da shi ya ce kasashen waje ba za su bari a zauna lafiya ba domin suna son su rika hakar ma'adinai a Najeriya
- Dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 ya ce Buhari ya yi kokari sosai wurin tabbatar da Najeriya a matsayin kasa daya duk da barazanar yan ta'addan
Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross Rivers, a ranar Alhamis ya ce dimbin ma'adinan kasa da Najeriya ke da shi yasa yan ta'adda ke zuwa kasar, rahoton Daily Trust.
Yayin da ya ke magana a Sunrise Daily a Channels TV a safiyar ranar Alhamis, Ayade ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Matsalar tsaro na da fuskoki da dama.
"Najariya na da ma'adinan kasa masu yawa da ake sayar da su da tsada. Don haka, ma'adinan na kasa ya zama wa kasar kallubalai.
"Najeriya tana da tantalite, lead, zink, gwal, da uranium sosai. Mafi yawan lokaci a Afirka idan kana da ma'adinai, matsala ya ke zama su (yan kasar waje) za su cigaba da janyo rikici domin su cigaba da hakar ma'adinan.
"Rushewar Afghanistan ya na nufin ISWAP sun yi wa Najeriya kallon yanki da Allah ya basu."
Ya ce burinsu shine kashe dukkan mazauna yankin domin suna ganin musulmin da kirista duk a matsayin arna.
Buhari ya taka rawar gani wurin tsaro, in ji Ben Ayade
Ayade ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kokarin tabbatar da cewa Najeriya ta cigaba da zama a matsayin kasa daya duk da hare-haren.
A cewarsa, kallubalen tsaro a Najeriya baya nufin rashin shugabanci nagari sai dai wani kallubale ne da ya shafi duniya baki daya.
A baya-bayan nan Ayade ya ayyana niyarsa na yin takarar shugaban kasa a 2023, ya ce zai hada kai da wasu kasashen duniya don amfani da fasahar zamani ya yaki yan ta'addan.
2023: Osinbajo Ya Gama Biyan Sadaki, Ya Cancanta Ya Zama Sabon Angon Nigeria, In Ji Basaraken Ƙasar Yarbawa
A wani rahoton, Alake na kasar Egba, a Jihar Ogun, Oba Adedotun Gbadebo ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi biyayya don haka ya cancanci a zabe shi shugaban kasa a 2023, PM News ta ruwaito.
Vanguard ta rahoto cewa Gbadebo ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata, a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasar da ya kai masa ziyarar ban girma.
Osinbajo, wanda ya samu rakiyar Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tafi jihar ne domin tuntubar masu ruwa da tsaki game da takarar shugabancin kasarsa na 2023.
Asali: Legit.ng