Hotunan Ƴar Yi Wa Kasa Hidima Da Aka Gano Gawarta Cikin Mummunan Yanayi a Abuja Kwanaki Bayan Ɓacewarta

Hotunan Ƴar Yi Wa Kasa Hidima Da Aka Gano Gawarta Cikin Mummunan Yanayi a Abuja Kwanaki Bayan Ɓacewarta

  • An gano gawar yar yi wa kasa hidima da aka sanar da ta bace a Abuja inda aka lura an cire wasu sassan jikinta
  • An yi wa Stephanie Se-Ember Terungwa, mai ya daya, ganin karshe ne a ranar Alhamis 14 ga watan Afrilu da safe a Lokogoma, Abuja
  • Richard Iorliam, kawun yar yi wa kasa hidimar da aka kashe ya ce an sace Stephanie ne tare da yaronta mai shekara daya bayan ta tashi daga CDS

An gano gawar matar da aka yi wa ganin karshe a ranar Alhamis 14 ga watan Afrilu, kuma an cire wasu sassan jikinta.

A cewar kawunta Richard Iorliam, an sace Stephanie ne tare da danta mai shekara guda bayan ta tafi wurin halartar CDS amma daga bisani an tsinci yaron.

Kara karanta wannan

Magidanci ya cika bujensa da iska bayan matarsa ta haifa ƴan huɗu

Sanarwar da Jamiar JS Tarka da ke Makurdi, Jihar Benue ta fitar ya ce an tsinci Stephanie babu rai.

Hotunan Ƴar Yi Wa Kasa Hidima Da Ako Gano Gawarta Cikin Mummunan Yanayi a Abuja Kwanaki Bayan Ɓacewarta
Hotunan Ƴar Yi Wa Kasa Hidima Da Ako Gano Gawarta Cikin Mummunan Yanayi a Abuja. Hotuna: Photo Credit: Dataphyte, @instablog9ja
Asali: Facebook

Hukumar NYSCta yi martani

Direktan sashin watsa labarai na NYSC, Eddy Megwa, ne ya bayyana hakan cikin wata gajeruwar sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta gani, Eddy ya ce an fara bincike domin gano wadanda suka kashe Stephanie.

Ya ce:

"Hankalin hukumar NYSC ya kai ga wasu hotunan wani yar yi wa kasa hidima da ke yawo a dandalin sada zumunta da aka ce ta bata bayan tura ta birnin tarayya Abuja.
"An tsinci gawarsa sanya da Khaki na NYSC da wadonsa amma fuskarsa da rauni ta yadda ba a iya gane shi.

Kara karanta wannan

Na Ɗauka Barewa Ne: Mafarauci Ya Bindige Limamin Ƙauyensu Har Lahira a Osun

"Bayan hakan, hukumar ta yi rahoto zuwa ga hukumomin da suka dace domin a taimaka a tabbatar da gawar ko ta wanene. Daga baya, an tabbatar cewa gawar dan yi wa kasa hidimar ne da ya bace, Stephanie Se-Ember Terungwa, mai lamba FC/21B/5807.
"Ana cigaba da zurfafa bincike domin gano wadanda suka aikata wannan mummunan lamarin domin su girbi abin da suka shuka. Allah ya jikanta."

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164