Rayuwa tayi wahala: Budurwa yar shekara 70 da ke jiran masoyi na gaskiya ta magantu a bidiyo

Rayuwa tayi wahala: Budurwa yar shekara 70 da ke jiran masoyi na gaskiya ta magantu a bidiyo

  • Har yanzu Kazamaliza Verena mai shekaru 70 bata cire tsammani ba cewa za ta hadu da namijin da take mafarkin samu ba wanda zai yi rayuwar farin ciki da ita
  • Matar wacce ta manyanta ta bayyana cewa babu namijin da ya taba tunkararta da sunan soyayya ko kuma ya yi kwanciyar aure da ita
  • Verena wacce bata da iyaye da yan uwa ta koka cewa rayuwa tayi matukar wahala da radadi a gare ta

Soyayya ruwan zuma ce kuma har yanzu Kamaliza Verena bata yanke kauna da samun namijin da zai so ta har su more rayuwa tare ba.

Matar mai shekaru 70 bata taba tarayyar aure da ‘da namiji ba kuma bata taba yin saurayi ba a rayuwarta.

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abj-Kad: Daya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hannun 'yan bindiga

Rayuwa tayi wahala: Budurwa yar shekara 70 da ke jiran masoyi na gaskiya ta magantu a bidiyo
Rayuwa tayi wahala: Budurwa yar shekara 70 da ke jiran masoyi na gaskiya ta magantu a bidiyo Hoto: YouTube/Afrimax
Asali: UGC
“Har yanzu ni budurwa ce. Ban taba aure ba, ban taba kwanciya da namiji ba kuma ban san ya ake ji a idan an aikata haka.”

Verena ta koka a wata hira da Afrimax cewa yanayin gajartar halittan ta da matsalar rashin lafiya da take fama da shi na iya zama dalilin da yasa bata samu masoyi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar wacce take rayuwa ita kadai – bata da iyaye da yan uwa- illa wata karamar yarinya da ke taimaka mata tana da wani ciwo a fuskanta.

“Ina rayuwa mai cike da kunci saboda a kullun cikin rashin lafiya nake. Bani da kudin magani..”

Verena ta bayyana cewa muradin zuciyarta ne ta yi aure bayan ta cika shekaru 20 amma bata yi nasarar samun masoyi ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a

Isabel Gillum ya ce:

Kara karanta wannan

Farinciki ya zama bakin ciki: Bidiyon amarya da ta haukace ranar aurenta

“Kila kaddararta ce kawai, akwai mutane a duniya da suke gajejjeru, guragu, makafai da duk wani nau’in nakasa kuma suna da aure, amma kan batun kasancewa budurwa ba laifi bane domin tana rayuwa mai tsarki ba tare da yin fasikanci ba Allah ya san dalili. Ina fata da addu’an Allah ya aiko mata da miji nagari."

Olive Grace ta ce:

“Allah na bamu abun da muke so a lokacin da ya tsara. Da ta yi gaggawan shiga soyayya, da ba lallai ne Allah ya tsare mata rayuwarta har zuwa yanzu ba mu gode ma Allah kan haka.”

NOMBULELO T. Z. Made ya ce:

“Babu abun da ya same ki. Allah ya baki burin zuciyarki kuma ya yasa duk tsare-tsarenki su cimma nasara. Dan Allah ki tuna cewa kowa na da tsarin rayuwarsa mabanbanta. Mun jinjina kuma mun yaba maki.”

Bana yi kuma: Budurwa ta soke aurenta ana saura kwana 3 saboda sun samu sabani da angon nata

Kara karanta wannan

Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka

A wani labari na daban, wata budurwa mai suna Ada Uburu ta soke aurenta da masoyinta David Okike, saboda rikicin cikin gida da ya gibta a tsakaninsu, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Matashiyar ta bayyana cewa mai shirin zama angon nata ya fara cin zarafinta ne tun bayan da ya biya kudin sadakinta, inda ta kara da cewar ta dade tana shanye bakin ciki a tattare da soyayyarsu da nufin abubuwa za su daidaita.

Ada ta bayyana cewa akwai lokacin da saura kadan mai shirin zama mijin nata ya kasheta ba don yan uwa da makwabta sun gaggauta shiga Tsakani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng