Kaduna: 'Yan sanda sun yi ram da 'yan ta'adda 2 dauke da miyagun makamai
- Rundunar'yan sanda jihar Kaduna ta yi ram da wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne da bindiga kirar AK-47 guda biyu da carbin harsasai masu rai guda 32
- Kakakin rundunar ya bayyana yadda rundunar tayi amfani da dabarbarun sirri wajen damko daya daga cikinsu a karamar hukumar Giwa da kuma dayan a Tudun wada Zaria
- 'Yan sandan jihar sun bukaci jama'a da su basu hadin kai ta hanyar basu bayanai don rage ta'addanci a fadin jihar
Kaduna - Rundunar 'yan sanda jihar Kaduna ta bayyana yadda tayi ram da wasu mutum biyu da ake zargin 'yan ta'adda ne a cikin jihar, TVC News ta ruwaito.
Kakakin rundunar, Muhammad Jalige, a wata takarda da ya fitar ranar Laraba ya bayyana yadda aka kama wadanda ake zargi da bindiga kirar AK-47 guda biyu, carbin harsasai masu rai guda 32.
Ya kara da cewa, jami'an tsaron da suka yi amfani da dabarbarun sirri sun damko daya daga cikin wadanda ake zargin , mai shekaru 25 cikin karamar hukumar Giwa dake jihar.
Punch ta ruwaito cewa, na biyun kuwa an kama shi ne a Tudun wada dake karamar hukumar Zaria, duk a jihar Kaduna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rundunar 'yan sanda jihar Kaduna ta bukaci jama'an dake yankin da su dunga bai wa rundunar bayanai game da duk wani abu da basu yarda da shi ba don rage ta'addanci matuka a cikin jihar.
Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Leggi Jibrin, ya shiga hannun sojojin Najeriya
A wani labari na daban, fitaccen gagararren shugaban kungiyoyin ta'addancin da suka addabi yankunan jihohin Benue, Nasarawa da Taraba, Leggi Jibrin, ya shiga hannun jami'an tsaro bayan artabun musayar wuta da yayi da dakarun sojin rundunar Operation Whirl Stroke, rundunar tsaro ta hadin guiwa dake kula da jihohin uku.
Vanguard ta ruwaito cewa, an tattaro daga bakin majiyar tsaro, cewa dan bindigan da OPWS ta dade tana nema ya shiga hannun sojoji ne a kauyen Agam/Gidan Bawa dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa yayin da suka fita aiki.
Majiyar ta ce dakarun sun yi aikin ne a ranakun Laraba da Alhamis karkashin umarnin kwamandan rundunar, Manjo Janar Kevin Aligbe. Hakan yayi sanadiyyar ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su a Ugya dake karamar hukumar Toto ta jihar.
Asali: Legit.ng