Sallah: Wamakko Ya Biya Wa Fursunoni 50 Bashi Da Tara, Za Su Tafi Gida Su YI Sallah Da Iyalansu

Sallah: Wamakko Ya Biya Wa Fursunoni 50 Bashi Da Tara, Za Su Tafi Gida Su YI Sallah Da Iyalansu

  • Sanata Aliyu Wamakko, tsohon gwamnan Jihar Sokoto ya kubutar da mutane guda 50 daga gidan yari a Sokoto
  • Dama Wamakko ya saba yin hakan duk kwanaki 10 na karshen watan Ramadana inda ya ke biyan tara da bashin fursunoni don a sake su
  • Mai magana da yawun Wamakko ya ce mai gidan ya yi karamcin ne domin mutanen su samu damar zuwa gidajensu su yi bikin sallah tare da yan uwa da abokan arziki

Sokoto - Sanata Aliyu Wamakko, mai wakiltan Sokoto ta arewa ya kubutar da fursunonin gidan yari su 50 daga gidan gyaran hali na Sokoto, rahoton Daily Nigerian.

An saki fursunonin ne bayan Wamakko ya biya musu tara da basusuka da ake bin su.

Sallah: Wamakko Ya Biya Wa Fursunoni 50 Bashi Da Tara, Za Su Tafi Gida Su YI Sallah Da Iyalansu
Sallah: Wamakko Ya Biya Wa Fursunoni 50 Bashi Da Tara. Hoto: Daily Nigerian.

Mr Wamakko ya saba irin wannan duk kwanaki 10 na karshen azumin watan Ramadan don saukaka wa mutane wahalhalun da suke ciki, NAN ta rahoto.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

Yayin da ya ke sakin fursunonin, Jami'in walwala a gidan gyaran hali na Sokoto, ASP Ayyuba Alhassan, ya yaba wa Wamakko saboda cigaba da wannan karamcin duk shekara.

Mai magana da yawun Wamakko, Hassan Sanyinnawal, a ranar Laraba a Sokoto ya ce cikin mutanen 50 da aka samawa yanci guda shida mata.

An saki fursunoni 35 daga gidan gyaran hali na birnin Sokoto yayin da sauran kuma daga gidan gyaran hali na garuruwan da ke kewaye ne karkashin sa idon gidan yarin na Sokoto, ya yi bayani.

A sakonsa, Wamakko ya yi bayanin cewa ya yi wa fursunonin karamcin ne domin su samu damar zuwa gida su yi sallah da iyalensu tare da rage cinkoso a gidajen yari.

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

Kara karanta wannan

Sarkin mawaka ko sarkin hauka - Babanchinedu ya yiwa naziru wankin babban bargo kan Nafisa Abdullahi

A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motarsa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel