Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun kashe shugaban tsagin jam'iyyar APC a Bayelsa
- Jam’iyyar APC a jihar Bayelsa ta yi rashin daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar ta, Sunday Frank-Oputu
- An kashe Frank-Oputu a gidansa a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari
- Rahoton da muka samo daga majiyoyi ya bayyana yadda 'yan bindigan suka samu damar hallaka shi
Bayelsa - Wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe wani shugaban tsagin APC a jihar Bayelsa Sunday Frank-Oputu.
The Nation ta tattaro cewa an kashe Frank-Oputu, dan kabilar Igbomotoru ne a karamar hukumar Ijaw ta Kudu, a daren ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, a gidansa dake Yenezue-gene a Yenagoa.
Jaridar ta ruwaito cewa, ana zargin cewa maharan sun harbe shi ne ta tagar gidansa da ke bude don samun iskar Allah saboda babu wutar lantarki a unguwarsu.
Frank-Oputu na daya daga cikin wadanda suka fafata wajen gano ingancin taron gangamin APC na mazabu a Bayelsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wancan lokacin ya kuma yi Allah-wadai tare da bibiyar harin da aka kai wata babbar kotu inda aka jefi alkalin kotun, Mai shari’a Nayai Aganaba da kwalabe.
'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna inda suka kashe mutanen yankin da kuma shugaban jam’iyyar APC na gundumar Aribi, Mista Iliya Auta.
Ko da yake rundunar ‘yan sanda ba ta mayar da martani kan lamarin ba, amma majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a daren ranar Litinin, inda suka kashe mazauna garin tare da jikkata da dama.
Vanguard ta ruwaito cewa, wata majiya ta ce:
"‘Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane da kuma sace dabbobi. Daya daga cikin wadanda aka kashen wani jigo ne na jam’iyyar mai mulki, shugaban jam’iyyar APC na gundumar Aribi, Iliya Auta."
Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m
A wani labarin, 'yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai aikin taimakon jama’a, Ramatu Abarshi, da diyarta Amira, bayan sun gama raba kayan fitan sallah ga al’umman garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa yan bindigar sun farmake su ne a ranar Asabar da rana a kusa da Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kachia, a yankin kudancin Kaduna, Daily Nigerian ta rahoto.
Misis Abarshi, tsohuwar shugabar sashen Injiniyan Lantarki na kwalejin jihar Kaduna, ta yi suna sosai wajen aikin taimakon jama'a da shirin zaman lafiya a kudancin Kaduna.
Asali: Legit.ng