Ba don namijin kokarin Buhari ba da matsalar tsaron Najeriya ta fi haka muni, Ayade

Ba don namijin kokarin Buhari ba da matsalar tsaron Najeriya ta fi haka muni, Ayade

  • Gwamnan Ben Ayade na jihar Kuros Riba ya ce jajircewar Buhari a ɓangaren tsaro ya sa abun bai fi haka muni ba
  • Gwamnan, wanda ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa, ya ce a baya har cikin birnin Abuja ana dasa Bam kuma ya tashi
  • Ayade ya kuma yaba wa shugaban ƙasa bisa namijin kokarinsa wajen kwato duk wasu yankuna dake hannun yan ta'adda

Abuja - Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya ce matsalar tsaron Najeriya zata iya fin haka muni in ba don namijin kokarin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ba.

Ayade ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da Buhari ranar Talata, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani gwamnan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamna Ben Ayade da shugaban ƙasa.
Ba don namijin kokarin Buhari ba da matsalar tsaron Najeriya ta fi haka muni, Ayade Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Gwamnan ya kuma yaba wa shugaban ƙasa bisa gano bakin zaren kaluben tsaro na ƙasa da ƙasa da na cikin gida, har ya samu nasarar murƙushe Boko Haram da yan bindiga.

Daily Trust ta ruwaito Ayade ya ce:

"Da Shugaba Muhammadu Buhari ba shi ne shugaban Najeriya ba da abun ya fi haka muni. Ina faɗin haka da cikakken kwarin guiwa saboda ina tuna lokacin da muke samun tashin bama-bamai har nan a Abuja."
"Duk wata tuta da ƙungiyar Boko Haram ta kafa a jihohin arewa maso gabas sai da aka kwantar da su ƙasa. Wannan ba zai hana kai hari nan da can ba, shekara 30 zuwa 40 aka shafe ana yaƙin Guerrilla."
"Abun da ya faru da Afghanistan ya jawo barazana ga tsaron ƙasar nan kuma al'amura suka ƙara taɓarɓarewa a arewacin Najeriya tare da manufar ISWAP na mamaye yankin Afirka ta yamma."

Kara karanta wannan

N-Power: Bayan umarnin Buhari zamu ƙara daukar matasa 13,823 a rukunin C a wannan jihar, Sadiya Farouq

Zan nemi takara a 2023 - Ayade

Bugu da ƙari, gwamnan ya ce zai nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe bayan shugaba Buhari ya amince masa.

Sai dai duba da yunkurin APC na jawo hankalin Jonathan ya yi takara, Gwamnan ya ce yana ganin girman tsohon shugaban ƙasa, kuma zai yi biyayya ga duk abin da shugabannin jam'iyya suka yanke.

A wani labarin kuma Sanata Orji Kalu, ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce be janye daga burinsa ba kuma ba zai taɓa janye wa ba

Sanata Orji Kalu ya musanta raɗe-raɗin dake yawo cewa ya janye daga takarar shugabam ƙasa karkashin APC a zaɓen 2023.

Sanatan ya ce yana nan daram kan bakarsa ta neman kujera lamba ɗaya, kuma ba zai taɓa janye wa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262