'Ba zan taba janye wa ba' Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC ya yi amai ya lashe

'Ba zan taba janye wa ba' Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC ya yi amai ya lashe

  • Sanata Orji Kalu ya musanta raɗe-raɗin dake yawo cewa ya janye daga takarar shugaban ƙasa karkashin APC a zaɓen 2023
  • Sanatan ya ce yana nan daram kan bakarsa ta neman kujera lamba ɗaya, kuma ba zai taɓa janye wa ba
  • A cewarsa tun daga 1999, yankin kudu maso gabas ne kaɗai ba su ɗanɗana mulki ba, don haka a yi musu adalci

Abia - Sanata Orji Uzor-Kalu ya ce be janye daga takarar shugaban ƙasa ba kamar yadda wasu kafafen watsa labarai ke yaɗawa.

Sanatan ya ce zai nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a APC idan har jam'iyya ta yanke kai tikitin takara yankin kudu maso gabas, kamar yadda Punch ta rahoto.

Sanata Kalu.
'Ba zan taba janye wa ba' Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC ya yi amai ya lashe Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kalu ya yi karin haske kan sanarwan da ya fitar ranar Talata, ya jaddada cewa matuƙar daidaito za'a yi to ya kamata a mara wa kudu maso gabas baya ta samu tikitin takarar kujera lamba ɗaya.

Kara karanta wannan

2023: Mutumin da Shugaba Buhari ke son ya gaje shi zai ba kowa mamaki, Sanatan dake son takara

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Matsaya ta a bayyane take, ban janye kudirin takarar shugaban kasa na ba kuma ba zan taɓa janye wa ba. Ina rokon yan uwana da suka fito takara daga kudu-kudu, kudu-yamma, sun janye su goyi bayan mu saboda daidaito."
"Idan har za'a yi adalci, kamata ya yi shugaba na gaba ya fito daga kudu maso gabas saboda yankin ne kaɗai bai ɗanɗana mulki ba tun 1999. Be dace wani ɗan kudu-kudu, kudu-yamma ya fito ba idan za'ai adalci."
"Jonathan ya kwashe shekara 6, Obasanjo shekara 8, ga kuma Yemi Osinbajo zai shekara 8 a mataimaki, idan har akwai adalci yanzun lokacin mu ne, kudu-gabas ya kamata a mara wa baya."

Wane mataki zasu ɗauka a siyasance?

Sanata Kalu ya ƙara da cewa sun fara tattaunawar samun maslaha da goyon baya saboda har yanzun shugaba Buhari bai goyi bayan kowa ba.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Sallah: Yan bindiga sun kashe Kwamandan jami'an tsaro, sun tarwatsa mutanen gari a Zamfara

"Duk wanda ya je wurinsa yana faɗa masa ya je ya yi shawara da mutanensa. Ni ban gaya masa zan nemi takara ba saboda har yanzun ba'a yanke kai tikiti kudu maso gabas ba."

A wani labarin kuma Wani gwamnan APC ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba ya ce shugaban ƙasa Buhari ya amince masa ya nemi shugaban ƙasa a 2023.

Jim kaɗan bayan gana wa da Buhari a Abuja, gwamnan ya ce zai fito takara ne amma ba wai dole shi za'a ba tikiti ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel