Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

  • Wani rahoto da ke fitowa daga jihar Kaduna ya bayyana cewa, an hallaka wani shugaban jam'iyyar APC
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu 'yan bindiga suka kai hari wani yanki, suka sace mutane da shanu da dama
  • Rahoton ya ce an kashe mutane da dama a yankin, lamarin da ya faru a jiya Litinin 25 ga watan Afrilu

Jihar Kaduna Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna inda suka kashe mutanen yankin da kuma shugaban jam’iyyar APC na gundumar Aribi, Mista Iliya Auta.

Ko da yake rundunar ‘yan sanda ba ta mayar da martani kan lamarin ba, amma majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a daren ranar Litinin, inda suka kashe mazauna garin tare da jikkata da dama.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa a PDP, Tambuwal

'Yan bindiga sun yi barna a Kaduna
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kashe shugaban APC a yankin Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito cewa, wata majiya ta ce:

"‘Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane da kuma sace dabbobi. Daya daga cikin wadanda aka kashen wani jigo ne na jam’iyyar mai mulki, shugaban jam’iyyar APC na gundumar Aribi, Iliya Auta."

Wata majiya ta bayyanawa jaridar BluePrint cewa, 'yan bindigan basu da niyyar hallaka Iliya ba, kawai dai sun zaci yana kira kami'an tsaro ne yayin da suka ga yana waya a cikin gonarsa.

Ya zuwa yanzu dai hukumomi basu tabbatar da faruwar lamarin ba, amma muna biye don kawo muku cikakken bayani.

Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m

A wani labarin, 'yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai aikin taimakon jama’a, Ramatu Abarshi, da diyarta Amira, bayan sun gama raba kayan fitan sallah ga al’umman garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa yan bindigar sun farmake su ne a ranar Asabar da rana a kusa da Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kachia, a yankin kudancin Kaduna, Daily Nigerian ta rahoto.

Misis Abarshi, tsohuwar shugabar sashen Injiniyan Lantarki na kwalejin jihar Kaduna, ta yi suna sosai wajen aikin taimakon jama'a da shirin zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.