Ramadan: Tinubu, Nyako da jiga-jigan APC 15 da za su yi buda baki tare da Buhari a yau

Ramadan: Tinubu, Nyako da jiga-jigan APC 15 da za su yi buda baki tare da Buhari a yau

  • Wasu jiga-jigan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC mai mulki na ta gagarumin yunkurin samun karbuwa gabanin zabe mai zuwa na 2023
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin jigon jam'iyyar APC na kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, Bisi Akande da sauran su a fadarsa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta karbi bakuncin 'yan takarar shugaban kasa a liyafar buda baki a fadar Villa

A yammacin ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai karbi bakuncin wasu shugabannin jam’iyyar APC a liyafar buda baki a fadarsa da ke Abuja.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wata takarda da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari ya aike wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce za a fara buda bakni da karfe 6:30 na yamma.

Kara karanta wannan

Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC

Fadar shugaban kasa: Buhari zai gana da su Tinubu
Tinubu da wani jigon APC za su yi buda baki tare da Buhari a Villa | Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

A cewar takardar gayyata da jaridar The Punch ta gani, wadanda aka gayyata taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu.

Hakazalika da tsaffin shugabannin jam’iyyar APC na kasa, Dr. John Oyegun, da Adams Oshiomhole da tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako.

Masu ruwa da tsaki ne na jam’iyya mai mulki da dama za su halarta

Ana kuma sa ran wasu jiga-jigan APC za su halarci liyafar, sun hada da:

1. Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba

2. Shugaban riko na farko na jam'iyyar APC, Bisi Akande

3. Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu-Sheriff

4. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Yarima

5. Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Wamako

6. Tsohon Gwamnan Jihar Edo, Oserheimen Osunbor

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

7. Tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Bukar Ibrahim

8. Janar Muhammed Magoro

9. Sanata Lawal Shuaibu

10. Aba Aji, Tijjani Tumsah

11. Fati Bala, Abubakar Guru, da

12. Nasiru Danu

Osinbajo, Tambuwal da sauran 'yan takarar shugaban kasa 10 da basu halarci taron Iftar din Aisha Buhari ba

A ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, ne uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta gayyaci yan takarar shugaban kasa a fadin jam’iyyun siyasa zuwa taron buda baki.

Yayin da wasu yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) suka amsa gayyatar, wasu basu halarci liyafar cin abincin daren ba.

Ga jerin manyan yan takarar shugaban kasa da basu halarci liyafar ba a wannan rahoton:

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.