Da Dumi-Dumi: Kotun Koli ta rushe halascin takarar Andy Uba na APC a zaben Anambra

Da Dumi-Dumi: Kotun Koli ta rushe halascin takarar Andy Uba na APC a zaben Anambra

  • Kotun Koli a yau Talata ta yanke cewa jam'iyyar APC ba ta da ɗan takara a zaɓen gwamnan Anambra da aka kammala
  • Kotun ta kuma tabbatar da hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara na soke takarar Andy Uba na jam'iyyar APC
  • Tun a watan Disamba 2021, Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta kori ƙarar tare da soke ingancin zaɓen APC

Abuja - Kotun Ƙoli ta rushe ingancin shiga zaɓen gwamnan jihar Anambra da Andy Uba ya yi a matsayin ɗan takarar jam'iyyar APC, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kotun yayin yanke hukunci ranar Talata, ta ce jam'iyyar APC ta saba wa dokokin ta wajen gudanar da zaɓen fidda gwani, bisa haka ba ta aiwatar da zaɓem fdda gwani mai sahihanci ba, wanda Andy Uba ya samu nasara.

Kara karanta wannan

APC ta samu babban cikas, dubbannin masoyan Buhari sun koma bayan takarar Kwankwaso a 2023

Andy Uba.
Da Dumi-Dumi: Kotun Koli ta rushe halascin takarar Andy Uba na APC a zaben Anambra Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta tabbatar da hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a ranar 23 ga watan Fabrairu, 2023, wanda ya goyi bayan hukuncin alkalin babbar Kotun tarayya, Mai Shari'a Inyang Ekwo.

Kotun Kolin ta kuma yi watsi da ƙarar da Andy Uba ya ɗaukaka a gabanta tare da jam'iyyar APC mai lamba SC/CV/240/2022 da SC/CV/241/2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A hukuncin babbar Kotun tarayya na 20 ga watan Disamba, 2021, ta yanke cewa Andy Uba ba shi ne halastaccen ɗan takara karkashin inuwar APC a zaɓen 6 ga watan Nuwamba, 2021.

Hukuncin ya nuna cewa APC ta tsayar da Uba ne ta hanyar zaben fidda gwani da ya saba wa doka.

Alkalin Kotun mai shari'a Justice Ekwo, ya yanke cewa mai shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/648/201, George Moghalu, (ɗan takarar APC) ya gabatar da sahihan hujjoji APC ba ta gudanarda zaɓen fidda gwabi mai inganci ba.

Kara karanta wannan

2023: Abinda zamu yi wa Bola Tinubu da a PDP yake neman shugaban ƙasa, Gwamnan Arewa

A wani labarin kuma APC ta samu babban cikas, dubbannin masoyan Buhari sun koma bayan takarar Kwankwaso a 2023

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu gagarumin goyon baya a shirinsa na gaje Buhari a 2023.

Wata ƙungiyar yan a mutun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta tabbatar da goyon bayanta ga jagoran Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel