Sadau, Nafisa, ‘Yan wasan Kannywood 7 da suka taba tada kura a shafukan sada zumunta

Sadau, Nafisa, ‘Yan wasan Kannywood 7 da suka taba tada kura a shafukan sada zumunta

  • Taurarin wasan kwaikwayo a kusan ko ina a fadin Duniya sun yi kaurin-suna wajen jawo surutu
  • Wasu ‘Yan Kannywood da suke tashe a Arewacin Najeriya su kan samu kan su a irin wannan yanayi
  • A kwana-kwanan-nan labarin Nafisa Abdullahi ake ta yi saboda ta soki dabi’ar rashin kula da ‘ya ‘ya

A wannan rahoto, Daily Trust ta kawo wasu daga cikin fitattun ‘yan wasan fim da taurarin mata da suka jawo surutai saboda wani abin da suka yi.

Legit.ng Hausa ta bibiyi rahoton, ta kuma kara da jerin wasu taurarin da ake ganin sun jawo abin magana a wajen harkar fina-finai da aka san su da ita.

1. Nafisa Abdullahi

Ta farko a jerin ita ce Nafisa Abdullahi wanda har yanzu maganar ta ake yi a Arewacin Najeriya tun da ta ce a daina haihuwar yaran da ba za a iya kula da su ba.

Kara karanta wannan

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

Wasu sun dauki wannan maganar a matsayin sukar Almajiranci da kokarin fito-na-fito da addini. Amma dai ‘yar wasar ta yi karin haske a kan abin da ta ke nufi.

2. Rahama Sadau

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kusan babu mai jawo maganganu irin Rahama Sadau. A 2016, sai da lamarin ya kai aka haramta mata yin fim a Kannywood saboda fitowa da tayi a wata waka.

Haka zalika bini-bini ta kan daura wasu irin hotuna da ake ganin sun sabawa addini da al’adar ta. Sadau ta na da dinbin mabiya a shafukan Twitter da Instagram.

3. Fati Slow

Fati Usman ta na yawan shiga labarai a kafofin sadarwa na zamani a kwanakin nan, musamman bayan ta yi wani bidiyo a shafin Tik Tok ta na sukar Sarkin Waka.

‘Yar wasar da aka fi sani da Fati Slow ta ba Naziru Ahmed hakuri bayan ya ba ta kyautar kudi. A makon nan aka ji tana sukar Nafisa yayin da ta ke kare mawakin.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Sadau da Gabon
Rahma Sadau da su Hadiza Gabon Hoto: @Rahma_sadau
Asali: Twitter

4. Hadiza Gabon

A shekarun baya an samu hatsaniya tsakanin Hadiza Gabon da kuma Amina Amal har aka ga Gabon ta na dukar ‘yar wasar a wani bidiyo da ya shiga Instagram.

Gabon tayi ikirarin Amal tayi mata sharri ne, daga baya dai an sasanta ‘yan wasan biyu. A wasu lokuta 'yar wasar kan yi martani mai zafi ga masu sukar ta a Twitter.

5. Sadiya Haruna

Sadiya Haruna tana cikin jaruman Kannywood da sun saba tada kura. Jaridar ta tuna cewa a kan jifan Isa A. Isa da sharri ne kotu ta yanke mata hukuncin dauri.

6. Maryam Yahaya

Kwanakin baya aka ga Maryam Yahaya a wani bidiyo ta na bayanin cewa ba ta da lafiya. Wannan faifai ya girgiza masoyar ‘yar wasar kwaikwayon mai shekara 24.

Bayan nan sai aka gan ta a birnin Dubai, har ta daura wasu hoto da suka jawo aka yi ta sukar ta.

7. Maryam Booth

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

A 2020 aka yi ta yada cewa an fitar da bidiyo da yake dauke da tsiraicin Maryam Booth. Wannan badakala ta jawo surutu tsakanin jama’a a shafukan sada zumunta.

Naziru ya yi habaici

Shahararren mawakin nan, Naziru M. Ahmed ya yi rubutu da ake ganin tamkar habaici yake yi saboda Nafisa Abdullahi ta soki haihuwar 'ya 'ya ba tare da kula ba.

An ji tauraron yana cewa almajiranci da iyaye suke aika yara ya na da amfani, kuma irinsa sun ci moriyar hakan, sannan ya yi kaca-kaca da wadanda ke harkar fim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel