Da dumi-dumi: Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Graham Douglas, ya mutu

Da dumi-dumi: Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Graham Douglas, ya mutu

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama na kasa, Alagbo Graham Douglas, ya kwanta dama
  • Douglas wanda ya rike mukamin minista sau biyu ya mutu ne a safiyar yau Litinin, 25 ga watan Afrilu, a babbar birnin tarayya, Abuja
  • An tattaro cewa kafin mutuwar nasa, marigayin ya sha fama da rashin lafiya na tsawon wani lokaci

Ribas - Labari da ke zuwa mana a yanzun nan shine cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama na kasa, Alagbo Graham Douglas, ya mutu.

Wani makusancin mamacin wanda ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust, ya ce Douglas ya mutu ne a Abuja a safiyar ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu.

Marigayin ya rike mukamin minista sau biyu sannan ya kuma kasance kwararre a bangaren hulda da jama’a.

Kara karanta wannan

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

Da dumi-dumi: Tsohon ministan sufurin jiragen sama ya rasu a Abuja
Da dumi-dumi: Tsohon ministan sufurin jiragen sama ya rasu a Abuja Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wani babban basaraken kabilar Kalabari a Ribas inda marigayi ministan ya fito, Cif Ngo Martins Yellowe, shi ma ya tabbatar da mutuwar tsohon ministan a Port Harcourt, babban birnin Ribas.

Yellowe, wanda ya kasance shahararren dan jarida, ya ce marigayin ya dauki tsawon wani lokaci yana rashin lafiya.

Ya kasance ministan raya al’umma da sufurin jiragen sama a gwamnatin Ibrahim Babangida sannan ya rike mukamin ministan al’adu da yawon bude ido da kuma na kwadago da samar da ayyukan yi a mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Duniya kenan: ‘Dan Majalisar Tarayya ya rasu kwatsam, ana shirin fara lissafin 2023

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa a ranar Lahadi, 24 ga watan Afrilu 2022 mu ka samu labarin mutuwar daya daga cikin ‘yan majalisar wakilan tarayya da ke Najeriya, Nse Ekpenyong.

Kara karanta wannan

Iftila'i: Wasu sun tsere, wasu sun jikkata yayin da coci ya ruguje kan masu ibada

Ana tunanin Honarabul Nse Ekpenyong mai shekara 58 a Duniya ya rasu ne a ranar Asabar. Jaridar Premium Times ce ta fitar da wannan rahoton a jiya.

Kafin rasuwarsa, Hon. Nse Ekpenyong shi ne mai wakiltar mazabar Oron a majalisar wakilan tarayya a karkashin babbar jam’iyyar hamayya watau PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel