Iftila'i: Wasu sun tsere, wasu sun jikkata yayin da coci ya ruguje kan masu ibada

Iftila'i: Wasu sun tsere, wasu sun jikkata yayin da coci ya ruguje kan masu ibada

  • Rahoton da ke isowa daga jihar Legas ya bayyana cewa, an samu hargitsi yayin da coci ya ruguje a jihar Legas
  • Rahoton ya ce akalla mutane shida suka samu munanan raunuka, inda wasu suka tsere daga cikin cocin
  • Wani da lamarin ya rutsa dashi ya magantu da manema labarai, inda ya bayyana yadda lamarin ya faru

Jihar Legas - Wasu mabiya addinin kirista a Cocin Deeper Life da ke unguwar Iragbo a Badagry taJihar Legas, sun samu raunuka a jiya Lahadi yayin da ginin cocin ya rufta.

A cewar rahoton NAN, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya inda ginin cocin ya rufta da misalin karfe 9:30 na safe yayin da ake ci gaba da hidimar coci ta ranar Lahadi.

Yadda coci ya rufta kan jama'a
Iftila'i: Wasu sun tsere, wasu sun jikkata yayin da coci ya ruguje kan masu ibada | Hoto: thecable.ng

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, ba a sami asarar rai ba a lamarin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Wani mamban cocin Topohozin Tunde ya bayyana cewa wasu ’yan cocin shida sun samu munanan raunuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Nima na samu wani mummunan rauni a gwiwa, amma mun gode Allah ba a rasa rai ba.
“Da misalin karfe 9:30 na safiyar yau, a lokacin da ake gudanar da ibada, an yi wata guguwa mai karfi wadda ta afkawa ginin cocin, kuma kafin mu ankaraa, ginin cocin ya ruguje.
“Wasu sun iya tserewa, yayin da mu kusan shida muka samu munanan raunuka.
“Wadanda suka samu munanan raunukan an kai su babban asibitin Badagry domin samun kulawar da ta dace.
"Tunda rauni na ba mai girma bane, na yanke shawarar kula da kaina."

Tunde, ya yi zargin cewa duk da cewa wadanda suka jikkata sun samu kulawar likitoci, ba a kula da su yadda ya kamata ba saboda “babu wani likita a asibitin” a lokacin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda fasinja ta yanke jiki ta fadi, tace ga garinku a filin jirgin sama dake Abuja

Shima da yake magana kan lamarin, Thoma Agodi, mai sarautar gargajiya na yankin Iragbo, ya ce yana cikin fadar sa ne wani mazaunin garin ya zo ya shaida masa cewa ginin cocin ya rufta, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce:

"Dole ne mu gode wa Allah da ba a samu asarar rai ba sakamakon rugujewar."

Kyakkyawan karshe: Yadda mutuwa ta dauki matashin Limami a tsakiyar Sujadar Tahajjud

A wani labarin, Legit.ng Hausa ta samu labarin rasuwar wani Alaranma mai suna Sani Lawal wanda ya rasu a lokacin da yake ibadar sallar dare a watan Ramadan.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga majiyoyi da dama, Sani Lawal ya rasu ne a daidai lokacin sujada, yana limancin sallar tahajjud a ranar Asabar dinnan.

Tuni dai aka yi jana’izar marigayin dazu da safe da kimanin karfe 8:00 na safe a unguwarsu da ke Layin MB, Samaru, karamar hukumar Sabon Gari, Kaduna.

Kara karanta wannan

Iftala'i: Bam ya tashi a Taraba, mutane 3 sun mutu, wasu da dama sun jikkata

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.