Mutuwa dai dole ce: Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta riga mu gidan gaskiya
- Duniya dai dole a mutu, mace mafi tsufa a duniya Kane Kanaka ta bakunci kiyama bayan shafe shekaru 119 a duniya
- Kwanan nan Kane Tanaka 'yar kasar Japan ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta kuma a cewar danginta, ta kasance tana ciki da waje a asibiti kafin ta ci taliyar karshe
- Toshuwa dai na kunyar a kira ta wacce tafi tsufa a duniya, taken da wata mata Bafaranshiya, Jeanne Louise Calment ta rike wacce ta rasu tana da shekara 122
Japan - Matar da ta fi kowa tsufa a duniya a karshe dai ta bar duniyar; Kane Tanaka ta rasu a ranar 19 ga Afrilu, 2022 tana da shekaru 119.
Babban kwararre kan ilimin tsufa da lafiya (Gerontology) Robert Young ne ya ba da labarin mutuwarta, wanda kuma ya taka rawa wajen tabbatar da ba da rahoto kan Kane a matsayin mafi tsufa a duniya a 2019.
A ranar 13 ga Afrilu, dangin Kane sun yi rubutu a Twitter cewa an kwantar da ita a asibiti kuma akan sallame ta kana ta dawo.
Kundin tarihin duniya na Guinness ya ruwaito cewa an haifi Kane a ranar 02 ga Janairu, 1903, a matsayin diya ta bakwai ga Kumakichi da Kuma Ota.
Tsohuwar ta kasance a wani gidan hutawa a Fukuoka kuma inda take wasan alluna da yin lissafi
Kundin na Guinness ya ba ta takardar shaidar tsufa, kana da kyautar cakuleti a wani biki.
Wani sako da danginta suka yada a Twitter game da samun takardar sun ce ta ce:
"Na sami damar zuwa wannan nisa ne tare da goyon bayan mutane da yawa. Ina fatan za ku ci gaba da nishadi, kuma ku kasance cikin fara'a da kuzari."
Mai rikon fitar Olympic Tokyo a 2020
An zabi Kane a matsayin daya daga cikin masu rike da fitilar Tokyo 2020 na Torch Relay amma bata samu halarta ba saboda Korona.
Tsohuwar dai na kan hanyar zama mafi tsufa a cikin matan duniya, lakabin har yanzu mallakar wata Bafaranshiya ce, Jeanne Louise Calment wacce aka haifa ranar 21 ga Fabrairu, 1875, kuma ta rasu a ranar 04 ga Fabrairu, 1997, tana da shekaru 122 da kwanaki 164.
Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya shi ne Jiroemon Kimura dan kasar Japan wanda aka haife shi a ranar 19 ga Afrilu, 1897, kuma ya rasu yana da shekaru 116 da kwana 54, a ranar 12 ga Yuni, 2013.
An kashe mutum uku a wani rikicin yan daba kan budurwa a jihar Kwara
A wani labarin daban, mutum uku sun rasa rayuwarsu, wasu da dama sun jikkata ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara sanadin wata budurwa.
Daily Trust ta rahoto cewa kungiyoyin yan daba biyu ne suka gwabza da juna biyo bayan wani saɓani da suka samu kan mace.
Rahoto ya nuna cewa faɗan ya soma ne ranar Asabar. Wani mazaunin yankin, Alhaji Abdurrahman, ya shaida wa jaridar cewa faɗan ya kaure ne tsakanin yan daban tsagin Isale Oja da na tsagin Oja Oba a Offa.
Asali: Legit.ng