Dattawan Katsina sun nemi alfarma 1 a wajen Ministan Buhari kafin ya bar kan mulki

Dattawan Katsina sun nemi alfarma 1 a wajen Ministan Buhari kafin ya bar kan mulki

  • Katsina State Elders’ Forum ta bukaci a kammala kwangilar fadada hanyar Katsina zuwa garin Kano
  • Sakataren kungiyar dattawan na jihar Katsina, Alhaji Aliyu Sani Mohammed, shi ne ya yi wannan kira
  • Aliyu Sani Mohammed yana so Ministan ayyuka ya umarci ‘yan kwangila su karasa ragowar aikin titin

Katsina - Kungiyar Dattawan jihar Katsina, ta roki Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola ya duba batun aikin titin Kano-Katsina.

A wani rahoto da Vanguard ta fitar a ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu 2022, an ji Katsina State Elders’ Forum ta kai rokonta gaban Raji Babatunde Fashola.

Manyan na jihar Katsina su na so Ministan ya umarci ‘yan kwangila su koma kan aiki a wannan titin da yanzu an yi sama da watanni uku da daina aikinta.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga Ɗaya a Anambra

Ana kokarin fadada wannan titi domin daukar motoci da yawa, amma a yanzu an dakata da aikin.

Sakataren kungiyar Katsina State Elders’ Forum, Alhaji Aliyu Sani Mohammed ya yi hira da manema labarai a garin Katsina, inda ya dauko batun titin.

Aliyu Sani Mohammed ya shaidawa manema labarai cewa wannan aiki da an kai 65% ya tsaya cak, an yi watanni uku ba a ga ‘yan kwangila a kan titin ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hanyar Katsina
Titin Kano-Katsina da CCECC su ke yi Hoto: @ajuringelale
Asali: Twitter

Meyasa aiki ya tsaya?

A cewar sakataren kungiyar, ba su san gaskiyar dalilin tsaida wannan aiki ba, amma ana rade-radin kamfanin CCECC su na so a sallami na kan hanyar ne.

Akwai mutanen da za a ba kudi, a tada da su daga kan titin. Idan da gaske ne, muddin gwamnatin tarayya ba ta sallame su ba, ba zai yiwu a cigaba da aikin ba.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Gwamnati za ta iya maka ASUU a kotu idan aka gagara yin sulhu inji Minista

“Mun damu game da yadda aikin titin Kano-Katsina ya tsaya gaba daya, ‘yan kwangila sun ajiye motocinsu, sun yi gaba, ba tare da wani bayani ba.”
“A wani dalili za su yi watsi da muhimmin aikin nan. Kwangilar ta na da muhimmanci. Titin ne ya shiga jihohin Zamfara, Sokoto har kasar Nijar.”
“Saboda haka mu na rokon Ministan, ya taimaka ya fadawa ‘yan kwangila su dawo su cigaba da aikinsu. Abin da ya rage kusan 30-35% ne kurum.”
“Ya taimaka ya dawo da su domin su kammala wannan aikin a lokacin da ya kamata.” - Alhaji Aliyu Sani Mohammed

Siyasar APC na 2023

Ana da labari cewa Muhammadu Buhari zai rabawa Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, da Rotimi Amaechi gardamar tikitin APC kafin ayi zaben fitar da gwani.

Jam’iyyar APC ta kusa sanin wanda shugaban kasa yake goyon baya ya zama Magajinsa. A halin yanzu sama da mutum 10 su ke shirin takara a APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng