Garba Shehu: Sukar FG da Kukah ke yi ne ya kawo jinkirin isowar jiragen Super Tucano

Garba Shehu: Sukar FG da Kukah ke yi ne ya kawo jinkirin isowar jiragen Super Tucano

  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce sukar mulkin Buhari da Kukah ke yi ne sanadiyyar jinkirin isowar jiragen saman yaki da ta'addanci daga Amurka
  • Jiragen yakin saman sun iso ne a watan Oktoba 2021 bayan an shigar da bukatar samar dasu tun shekarar 2015, amma rikice-rikicen addini ya yi sanadin jinkirin isowar su
  • Haka yana da nasaba ne da yadda abokan adawan mulkin Buhari, wadanda suka sha kaye a zaben da ya gabata suka yi ta kara-kaina a Amurka

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya ce, sukar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da Rabaren Mathew Kukah ke yi yayi sanadiyyar jinkirin isowar jiragen yaki daga kasar Amurka.

A watan Oktoba 2021, gwamnatin tarayya ta sanar da yadda ake sa ran isowar jiragen saman yaki kirar A-29 guda 12 daga Amurka.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Garba Shehu: Sukar FG da Kukah ke yi ne ya kawo jinkirin isowar jiragen Super Tucano
Garba Shehu: Sukar FG da Kukah ke yi ne ya kawo jinkirin isowar jiragen Super Tucano. Hoto daga Garba Shehu
Asali: Facebook

A wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a shafinsa na Twitter, Shehu ya ce an bukaci shigo da jiragen saman ne a shekarar 2015, amma jinkirin isowar jiragen na da nasaba da yadda Amurka ta fara magana a kan rikice-rikicen addini a Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasan ya ce yawan kara-kainan a kasar Amurka da 'yan adawar mulkin Buhari "wadanda suka sha kaye a zaben da ya gabata" shima ya dagula lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda kakakin shugaban kasa ya ce, "mabiya addinai" wadanda suka hada da Matthew Kukah, babban limamin cocin katolika ta yankin Sakkwoto, na daga cikin "abokan adawan" gwamnatin tarayya.

"A shekarar 2015, gwamnatin Buharin da aka zaba ba da jimawa ba, ta bukaci agajin rundunar sojin Amurka da ta kawo dauki da jiragen yaki ga sojin saman Najeriya," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

"Haka zalika, sojin kasan Najeriya, jami'an tsaro da jami'an binciken sirri suka sake shigar da bukatar. Gwamnatin Amurka ta lokacin ta amince: shigo da irin jiragen yaki saman zai taimaka wajen ganin an kawo karshen 'yan ta'addan Najeriya da hamada.
"Shekaru biyu suka shude, amma jirage basu iso ba, dalilan da suka bada su ne, sai Najeriya ta gyara alaka tsakanin addinin kiristanci da na musulunci sannan Amurka zata kawo daukin da sauran yankuna.
"Sai dai kuma cikin sa'a, yanzu a yau karkashin sabon mulkin Amurka, wadannan jiragen yakin sun iso, kuma sun tashi hankalin 'yan ta'addan - tare da gawurtaccen shugaban ISWAP da sauran tarin shugabannin kungiyoyinsu duk an shekesu a luguden wuta.
"Abu ne mai kyau kusan da cewa, Amurka na da burin taimakawa Najeriya don ta fi haka a siyasa da tsayawa da kafafunta."

Daga karshe, Shehu ya kara da cewa, Amurka da Najeriya za su cigaba da abokantaka wajen "yaki da ta'addanci ciki da wajen yankuna."

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Jirgin sojin sama ya ragargaji maboyar 'yan bindiga a Taraba

Asali: Legit.ng

Online view pixel