Masu Garkuwa Sun Sake Kashe Wani Ɗan Kasuwan Kano Bayan An Biya Kuɗin Fansarsa

Masu Garkuwa Sun Sake Kashe Wani Ɗan Kasuwan Kano Bayan An Biya Kuɗin Fansarsa

  • Masu garkuwa da mutane sun sake halaka wani dan kasuwar Jihar Kano, Umar Sani (Magaji) bayan karbar kudin fansa
  • An sace Magaji ne tare da wasu matafiya biyar a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a hanyarsu ta zuwa Buruku kuma aka nemi iyalansu su biya fansa
  • Sai dai daga bisani bayan biyan fansar mutane biyar kadai suka sako, mutanen kuma suka tabbatar masu garkuwan sun kashe Umar Sani

Kano - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ka hanyar Kaduna-Birnin Gwari sun sake kashe wani dan kasuwan Kano, Umar Sani, bayan karbar kudin fansa daga yan uwansa, rahoton Daily Trust.

An sace dan kasuwan wanda ake kira Magaji ne kimanin makonni biyu tare da wasu mutane biyar a hanyarsu ta zuwa Buruku amma daga baya wadanda suka sace shi suka kashe shi bayan karbar kudin fansarsa.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga Ɗaya a Anambra

Masu Garkuwa Sun Sake Kashe Wani Ɗan Kasuwan Kano Bayan An Biya Kuɗin Fansarsa
Masu Garkuwa Sun Sake Halaka Wani Ɗan Kasuwan Kano Bayan An Biya Kuɗin Fansarsa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Marigayin dan asalin karamar hukumar Fagge ne a birnin Kano.

Dan Uwan Marigayin Ya Magantu Kan YaddaSuka Gano An Kashe Dan Uwansu

Yayan marigayin, Hussaini Sani, ya tabbatarwa Daily Trust rasuwarsa a ranar Juma'a, ya kuma ce masu garkuwar sun kira su a ranar Alhamis suna neman wani Naira miliyan 20 duk da cewa sun kashe dan kasuwan.

"Su tara aka sace su, an fara tattaunawa da iyalan mutum shida, daga baya muka yarda za mu biya baki daya, kawai sai muka ga mutum biyar sun dawo.
"Da muka tambaye su, sun tabbatar mana kashe masu garkuwan sun kashe shi. Mun kira su (masu garkuwan) ta lambar da muka yi magana da su kuma suka dage cewa dan uwan mu na da rai, har ma sun nemi karin wani kudin kafin su sako shi.

Kara karanta wannan

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

"Da muka dage cewa sai munyi magana dan uwan mu kafin mu sake biyan kudi sai suka fada mana cewa sun kashe shi, suna mai cewa ya yi yunkurin tserewa ne. Amma wadanda aka kama su tare sun ce da gangan aka kashe shi," in ji Hussaini.

Magaji ya bar matan aure daya da yara hudu, wanda a yanzu suke zaune a karamar hukumar Bichi, rahoton Naija Dailies.

Mutuwarsa na zuwa ne kwana 10 bayan an gano gawar wani dan kasuwar Kano a dajin Kogi bayan biyan Naira miliyan 6 don fansarsa.

An Tsinci Gawar Ɗan Kasuwar Kano Bayan Iyalansa Sun Biya N6m Ga Masu Garkuwa

A wani rahoton, iyalan Yahaya Hassan Musa, dan kasuwa mai shekaru 39, sun shiga zaman makoki bayan an gano gawarsa a wani daji awanni bayan wadanda suka sace shi sun karbi Naira miliyan 6 matsayin kudin fansa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Fitattun Attajirai biyu sun lale miliyan N200m zasu siyawa mutum biyu Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC

Lamarin ya samo asali ne a ranar Alhamis, a yayin da mutum wanda ke da aure da 'ya'ya biyu, ke dawowa daga Cotonou, inda ya tafi kasuwanci amma aka sace shi a wani daji da ke Mopa, Jihar Kogi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa da farko masu garkuwan sun nemi a biya su Naira miliyan 10 domin fansarsa daga bisani suka rage zuwa Naira miliyan 6.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164